Masu motocin alfarma na rokon na kasa kudin mai a Dubai

Masu motocin alfarma na rokon masu tafiya kasa kudin mai, a Dubai da ke kasar Hadaddiyar daular Larabawa. Don haka ’yan sanda Masarautar Dubai suka roki al’umma da su rik akai rahoton irin wadannan mutanen.Wakilin jaridar Gulfnews, ya gano wani mutum da ke tuka motar alfarma, wadda aka sanya wa lambar motar alamar tambaya aka […]

Masu motocin alfarma na rokon na kasa kudin mai a Dubai
Masu motocin alfarma na rokon na kasa kudin mai a Dubai

Masu motocin alfarma na rokon masu tafiya kasa kudin mai, a Dubai da ke kasar Hadaddiyar daular Larabawa. Don haka ’yan sanda Masarautar Dubai suka roki al’umma da su rik akai rahoton irin wadannan mutanen.
Wakilin jaridar Gulfnews, ya gano wani mutum da ke tuka motar alfarma, wadda aka sanya wa lambar motar alamar tambaya aka rufeta, ta yadda ba za a iya gane motar ba, inda mutumin ke rokon kudin mai.
Jaridar ta ruwaito masu motocin wadanda mafi yawansu suka fito daga kasashen yankin tekun Fasha (GCC), a cikin motocinsu na alfarma masu tsada, suka rika yin wani abin mamaki, inda suke rokon matafiya a kasa su ba su kudin da za su sayi man motarsu.
Mutane da dama a cikin birnin sun tabbatar da cewa masu motocin kan zo su tambaye su kudi, don su samu su koma gida. kungiyar Hadin Gwiwa ta kasashen Yankin Tekun Fasha (gulf Cooperation Council), ta hada kasashe kamar haka: Hadaddiyar Daular Larabawa da Saudiyya da Kuwait da katar da Bahrain da Oman.
A kalla mazaunan birnin hudu an nemi irin wannan bukatar a wajensu, inda wasu mutanem a cikin mota kirar Chrysler 300 da Ford Edplorer suka roki kudin mai a wajensu.
“Na cika da mamaki da na ga wani mutum a cikin sutura mai kyau, a wata mota koriya Bentley, wanda ya roke ni kudin mai don ya samu ya koma Saudiyya,” inji Rahaman, wani mai wankin tufafi a otal, lokacin da yake tafiya a kan hanya a kafa.
Wani ma’aikacin otal da ke aiki a kan titin Shaikh Zayed, ya bayyana cewa ya bai wa direban da ya roke Dirhami 70 (Naira 1,750).
Wani babban jami’in ’yan sandan Dubai, Kanar Ali Ahmad Ganem, da ke da ofis a Bur Dubai, ya roki al’umma da a rika kai rahoton irin wannan mutanen.
“Babu damuwa mutum ya yi roko a taimaka masa idan bukatarsa ta gaskiya ce, amma sai dai irin wadannan al’amura sun fi aukuwa ne a lokacin azumin watan Ramadan, inda kwararrun mabarata ke amfani da damarsu wajen karbar dimbin sadakar da mazaunan birnin ke bayarwa,” inji a hirar da ya yi da jaridar Gulf News.
Ya ce kwananan za a fara kai wa mabarata farmaki a daidai lokacin azumin Ramadan.

Abubuwan da ya kamata ku sani game da Zaɓen Edo

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu