Mawaki ya maka BBC Hausa a kotu, yana menan diyyar miliyan 120

Mawaki Abdul Kamal na neman diyyar miliyan 120 daga Sashen Hausa na BBC kan amfani da kidan wakarsa ba da izininsa ba

Mawaki ya maka BBC Hausa a kotu, yana menan diyyar miliyan 120

Wani mawakin Hausa mai suna Abdul Kamal ya maka Sashen Hausa na BBC a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Kano bisa zargin amfani da kidan wakarsa ta ‘Maryamu’ ba da izininsa ba.

Lauyan mawakin, Barista Bashir Ibrahim Umar ya shaida wa kotun cewa BBC suna amfani da kidan wakar Abdul a shirin su mai suna ‘Daga Bakin Mai Ita’ ba tare da izininsa ba, wanda hakan ke iya janyo masa matsala a harkar sana’arsa.

“Kasancewarsa mawaki mai tasowa, hakan na iya zama matsala gare shi domin wasu za su yi zaton shi ne ya dauki kidan daga BBC don neman shuhura ko wani abu makamancin hakan,” in ji lauyan nasa.

Don haka lauyan ya nemi kotun da ta dakatar da kafar BBC daga ci gaba da amfani da sautin kidan, ya kuma nemi kotun da ta tilasta BBC biyan Abdul Kamal diyyar Naira miliyan 120.

Sai dai lauyan BBC, Barista Shakirudden Mosobalage ya mayar da martani cewa BBC ta sayi sautin kidan ne daga hannun wani kamfani da ke zaune a Abuja.

Barista Shakirudden Mosobalage ya kuma roki kotun da ta ba su dama su gabatar mata da wasu takardu, rokon da kotun ta amince da shi.

Alkalin kotun, Mai sharia. N. M. Inusa ya dage sauraron shari’ar zuwa ranar 12 ga watan Disamba.