NAJERIYA A YAU: Rayuwar Maza Masu Fama Da Matsalar Rashin Haihuwa

Shirin Najeriya A Yau zai yi nazari ne a kan matsalolin da suke hana maza haihuwa.

NAJERIYA A YAU: Rayuwar Maza Masu Fama Da Matsalar Rashin Haihuwa

Rashin haihuwa matsala ce da ke wargaza gidajen aure da dama a wannan zamani.

Da an samu shekara biyu zuwa uku bayan an ɗaura aure ba tare da an samu ƙaruwa ba za a fara yamaɗiɗi da matar a kan ba ta haihuwa.

Sai dai likitoci sun ce maza ma ka iya fama da wannan larura saboda wasu dalilai.

Shirin Najeriya A Yau zai yi nazari ne a kan matsalolin da suke hana maza haihuwa.

Domin sauke shirin, latsa nan