Nakatarori Hadeja: Alhajin da ya shafe shekara 51 bai yi fashin aikin hajji ba

Alhaji Muhammadu Nakatarori Hadeja, mutum ne da ya shafe shekara 51 bai aba fashin aikin hajji ba. A hirar da ya yi da Aminiya, dattijon dan kimanin shekara tamanin,zai ci gaba da zuwa aikin hajji matukar Allah Ya ba shi lafiya a shekara mai zuwa. Ga dai yadda hirar ta kasance: Daga Abdullahi Anako a […]

Nakatarori Hadeja: Alhajin da ya shafe shekara 51 bai yi fashin aikin hajji ba
Nakatarori Hadeja: Alhajin da ya shafe shekara 51 bai yi fashin aikin hajji ba

Alhaji Muhammadu Nakatarori Hadeja, mutum ne da ya shafe shekara 51 bai aba fashin aikin hajji ba. A hirar da ya yi da Aminiya, dattijon dan kimanin shekara tamanin,zai ci gaba da zuwa aikin hajji matukar Allah Ya ba shi lafiya a shekara mai zuwa. Ga dai yadda hirar ta kasance:

Daga Abdullahi Anako a Makka da Abubakar
AbdurRahman Dodo a Abuja

Aminiya: Ko zaka bayyana mana tsawon lokacin da ka fara zuwa aikin hajji?
Alhaji Nakatarori: Na fara zuwa aikin hajji tun ana tafiya a mota, kafin a kawo jiragen sama, gabanin Najeriya ta samu ’yancin kai. Sai dai ban samu yin hajji a shekarar 1960 ba, saboda a lokacin da na isa Sudan ba ni da isassun kudi, don haka na dawo gida.
A wancan zamanin muna zuwa hajji ne ta Sudan. Na kan bi ta Ndjamena zuwa Libiya, inda nike yin aikin karfi, don kara guzuri a kan abin da nike da shi kafin in karasa zuwa Sudan. A lokacin ba a maganar biza, abin da kawai kake bukata shi ne izinin wucewa (Laissez Passer). Ibrahim Abooth shi ne jami’in kula da aikin hajji na Sudan a wancan zamanin.
A lokacin da aka bullo da zuwa aikin hajji ta jirgin sama, mutum 40 kawai ake iya dauka. Kuma a wancan zamanin babu rediyo, saboda haka idan jirgin zai zo, sai a yi amfani da kakaki, don sanar da zuwansa. Kudin tikitin zuwa hajji a zamanin ya kai kimanin Naira 250 ta yanzu. Alhamdulillahi, wannan shi ne hajjina na 51, kuma in Allah Ya yarda ina nan a raye cikin koshin lafiya badi ma zan koma.
Aminiya: A ina kake samun kudin da kake biyan aikin hajjinka a wannan zamanin?
Alhaji Nakatarori: Ni dan kasuwa ne, ina tara kudina ne. Kuma a daidai lokacin da nike Magana da kai, kudin aikin hajjina na badi sun cika. A halin yanzu na zo aikin hajjin ne a matsayin jami’in gudanarwar hukumar Alhazan Jihar Jigawa. Gwamna Sule Lamido ne ya nada ni, kuma ko ba na cikin hukumar zan ci gaba da zuwa. Zuwa hajji ya damfaru a cikin rayuwata. A hakikanin gaskiya shekarar da na kasa zuwa aikin hajji, har aikin dan doka na yi don in tara kudi na shekara daya, sannan na samu na yi aikin hajjin a shekarar da ta zagayo.
Aminiya: Ko za ka iya tuna wadanda kuka yi aikin hajji tare da su a wadancan shekarun ?
Alhaji Nakatarori: A Hadeja, babu daya daga cikin abokan aikin hajjina da ke raye, amma a Kano na yi aikin hajji tare da mutanen da suka hada da Baba danbappa da dan Kasim da Adamu Dogo Nawarure da Alhaji Maiwada da sauransu. A wancan zamanin danbappa da danKasim su ne agent masu kai mutane aikin hajji. Don babu hukumar alhazai a lokacin.
Gwamnatin Marigayi Janar Murtala Muhammad ce, ta kawar da ’yan kayi na yi (agent) a harkar aikin hajji, sannan ta bullo da hukumomin kula da jin dadin alhazai. Na kasance daya daga cikin jami’an hukumar alhazai ta Jihar Kano tun a shekarar 1975, zamanin Murtala.
Aminiya: Ko za ka bayyana mana irin ci gaban da aka samu a tsawon shekaru 50 da suka gabata, tun sa’adda ka fara ziyaratar birnin Makka?
Alhaji Nakatarori: A zamanin da na fara ziyarar dakin Ka’aba babu sumunti a jikinsa. Wurin dawafi kuwa cike yake da kananan duwatsu da balgatattun tubulai. Mukan yi kai-kawo a kan duwatsun mu yi dawafi. Kai hatta ruwan Zamzam wani ne Musa Zamzam ke raba shi a tulunan kasa. Shi ma titin zuwa Ka’aba a kan tsauni yake, don haka sai an hau kan tsaunuka ake isa wurin. Mun yi tafiya a kasa zuwa Minna da Arafa da wurin jifa (jamrat).
A wancan zamanin mukan dauki ’yan kayanmu da ganyen dabino a matsayin makarin rana. A wancan zamanin, har ma sa’adda aka bullo da amfani da jirgin sama, daukacin ’yan Najeriya da ke zuwa aikin hajjin ba su wuce mutum 350, amma a yau ko Jigawa tana dibar dubban mahajjata.
Aminiya: Wata nawa ake shafewa zuwa aikin Hajj a mota?
Alhaji Nakatarori: A kalla wata uku.
Aminiya: Wasu za su so jin cewa ka yi aikin Umra, sabanin yawan zuwa aikin hajji da kake yi?
Alhaji Nakatarori: Abokina, Umrah ta yara ce. Mazaje na hakika hajji suke zuwa. Idan har ba ku ganni a hajji ba, to ko dai wani ya hana ni zuwa ba, ko kuma a ce na tsufa. Baya ga haka na san cewa, Allah ne ke kiran mutane zuwa hajji. Idan ya kirani zan ci gaba da amsa kiransa.
Tun da na fara aikin hajji fiye da shekara 50 da suka wuce, sau biyu kawai na kasa zuwa. Na farko, kamar yadda na gaya maka, na kasa samun isassun kudi da za su karasa da ni daga Sudan zuwa Makka. Na biyu kuwa, shi ne kamun da aka yi wa Sule Lamido da Abubakar Rimi a shekarar 1998, domin tun a baya mu magoya bayan jam’iyyun NEHU da PRP ne, shi ya sa na ziyarce su a kurkuku.
Aminiya: Ko a wannan nisan shekarun naka ka fi bukatar tafiya Minna da wurin jifa a kasa?
Alhaji Nakatarori: Me zai hana? Ina da karfi da lafiya. Allah Ya albarka ce ni da lafiya. A duk lokacin da nake bukata, sai kawai in dauki jakata in kama tafiya.
Aminiya: Yaya kake ganin kanka a matsayin jami’in Hukumar Jin Dadin Alhazan Jihar Jigawa?
Alhaji Nakatarori: Ni Gwamna Sule Lamido ne ya nada ni. Na san shi tsawon lokaci, tun yana matashi, mai tsattsauran ra’ayi, wanda ba ya jin tsoron kowa.
Aminiya: Tunda a siyasance kai dan NEHU ne, mene ne matsayinka a halin yanzu?
Alhaji Nakatarori: Siyasa dai ta riga ta sauya matuka. Don haka babu abin da ya yi saura sai bambadanci da neman kudi.