Nazari: Mawaki Rarara da yankan kunkurun Bala (1)

Mazaunin wannan rubutu ya ginu ne bisa kokarin fahimtar yadda wasu ayyukan adabi a cikin kowace al’umma ke tsira da girma da kuma narkewa a cikin zukatan al’ummarsu da ma wadanda ke zagaye da su, musamman a Arewacin Najeriya daga rayuwar tashin- tashina da suke cin karo da ita, yau da kullum. Irin wadannan gungun […]

Nazari: Mawaki Rarara da yankan kunkurun Bala (1)
Nazari: Mawaki Rarara da yankan kunkurun Bala (1)

Mazaunin wannan rubutu ya ginu ne bisa kokarin fahimtar yadda wasu ayyukan adabi a cikin kowace al’umma ke tsira da girma da kuma narkewa a cikin zukatan al’ummarsu da ma wadanda ke zagaye da su, musamman a Arewacin Najeriya daga rayuwar tashin- tashina da suke cin karo da ita, yau da kullum. Irin wadannan gungun ayyukan adabi suna samuwa ne ba tare da wani shiri na musamman ba, ba kuma da wani tanadi da aka yi ba, suna wakana ne kurum duk lokacin da tura ta kai bango a cikin rayuwar al’umma.
Bincike ya nuna cewa su irin wadannan gungun ayyukan adabi sukan wanzu ne a cikin wani zamani da jama’a kan yi tutsu game da wata rayuwa da ba su amince mata ba. Ana samun wadannan ayyukan adabi ko dai a cikin tsarin siyasa ko ginuwar tattalin arziki ko tsara da gudanar da addinai ko kuma zamantakewa ta yau da kullum.
A nan ba za mu yi kandamau ba, wato mu jajibo dukkan zangunan tsarin rayuwar al’ummar Arewacin Najeriya ba, za mu yi wa kanmu turke da zango ko karnin da ya wuce, musamman lokacin mulkin mallaka da siyasar da ta auku bayan mulkin mallaka tsakanin jam’iyyar NPC da NEPU. Za mu zakulo daga wadansu wasiku da kasidu da jawabai da wakokin siyasa da aka gabatar a cikin wasu jaridu na wancan lokaci da kuma rubutattun wakokin siyasa daga marubutansu da kuma jam’iyyun da ke adawa. Za mu yi haka ne ta amfani da nazarin irin yadda al’umma ke ginuwa da yadda tsarin zamantakewar al’umma ke agazawa wajen rarraba al’ummar zuwa abokan adawa da kuma turke su a tsakanin wancan gwauron siyasar da marin waccan siyasar. Ta haka muke fatar za mu fahimci irin yadda wasu ayyukan adabi ke samuwa da kuma yadda suke taimakawa wajen fahimtar rayuwar al’ummma, musamman dangane da badakalar da wakokin Rarara suka tayar bisa la’akari da ganin mabambantan ra’ayoyi na goyon baya da suka da la’ana da damuwa da kuma batun shiga kotu ko yin ramuwa dangane da wannan aikin adabi.
Bari mu soma da batun canji da yadda yake gudana a cikin al’umma da kuma yadda wajen nemansa da kafa shi a kowane tsari na rayuwa sai an gwabza, an ba hammata iska, an je, an dawo, musamman daga masu hulda da ayyukan adabi. Malam Aminu Kano ya bayyana mana cewa canji “na nufin sauyi daga tsofoffin hanyoyin rayuwa da suka yi wa al’umma kangi, kuma suke sa mutum ya ji shi ba wata halitta ba ce mai daraja. Kuma duk lokacin da mutum ya nemi ya shawo kan ire-iren wadannan matsaloli (na kangi), sai a yi masa lakabi da dan tawaye. Sai dai a tuna a wannan lokaci shi wanda ke takure bai damu da ya tunkari tankunan yaki ba, idan hakan shi ne mafita a gare shi.” Ke nan neman canji ko sauyi ko gyarta lamurran rayuwa ba abu ne sabo ba, ya dade tattare da al’umma, wannan ke sa a shiga cikin halayen musayar yau da kattaba batutuwa da a lokutta da dama ba sa farantawa sai tseguntawa da bakantawa da alamun cin mutunci ga wasu, kamar yadda muke gani a halin yanzu.
Bincike-bincike da nazarce-nazarce da aka dade ana gudanarwa kan yadda al’ummu ke ginuwa, musamman a kasashe masu tasowa daga shekarun 1950 suna tafe ne da nasu kamannu mabambanta. Akwai masu kallon ginuwar al’ummar ta fuskar yanayin jan ra’ayin jama’a don su saje a matsayin tsintsiya madaurinki daya, a maimakon a tsaya a warwatse ta yadda abokan gaba ko adawa za su iya samun galaba a kansu da sauri, misalin irin wannan tsari ne aka samar a kasashe da tsarin mulkinsu na gargajiya ne ko kuma na zamani, inda shugabanci ke fadawa a hannun masu gari ko iyayen kasa ko kuma jam’iyyun siyasa, wannan ra’ayi shi ke tashe a fannin nazarin zamantakewa.
Saboda haka duk tsarin da bai da wata madogara ko wata majalisa da za ta kula da yadda ake samar da dukiya a kasar da yadda ake raba ta, to wannan tsari zai kasance tamkar tsarin mulkin wawaso ne, kowa ya dauki rabonsa. Wannan ne ya sa ko inda ake da tsarin mulki da jam’iyyun siyasu tsayayyu, murdiya da cin zabe ta hanyar zurmuke, hanyoyi ne na amsar mulki da kuma danne muryar adawa da kokarin tabbata bisa mulkin, ko da jama’a ba su so. A irin wannan tsari, adawa takan yi tsanani da zafi domin ba wanda ke son a kada shi a zabe, musamman a yawancin kasashen Afirika, wannan ne kan sa wasu kokowar kwatar mulki ta kowace hanya, shi ya sa ake ganin cewa dimokuradiyya a irin wannan tsari ba ta zauna da gindinta ba, sai mulkin kama karya. ’Yanci da ci gaban jama’a a wannan tsari ba shi aka sa gaba ba, balle ma a damu da shi.
Duk da cewa ra’ayoyi sun bambanta dangane da irin wannan halayya, abin da ke da muhimmanci bai wuce haka lallai na faruwa ba, wasu na tsine wa wadanda suke gallaza musa, wasu na murna ganin cewa mulki ya fado hannunsu ko da kuwa wannan ba zai taimaka wajen ci gaban dimokuradiyya ba, balle uwa-uba ginuwar tattalin arzikin kasa. Dagewa domin samun dorewa a mazaunan mulki ya zama dole ne ga wasu, domin ci gaban kasa da kyakkyawan tsarin dimokuradiyya abubuwa ne da yawancin jama’a ke kishirwar su, musamman a kasashe masu tasowa.
Yawancin kasashen Afirika sun shigo turbar zamananci ce daga mulkin gargajiya, sai dai an sami wadansu ’yan canje-canje, a wadansu sassan an sha ba-ta-kashi da wadanda ba su son zamananci, sun fi son a ci gaba da abin da aka gada. Bisa irin wannan tunani ne wasu masu mulki suka fara neman yadda za su dawwama bisa mulkin don jin dadin kansu, ko da kuwa sauran jama’a na cikin ukuba. Irin wannan tantagaryar rashin kunya da kwace da danniya rana tsaka ya sa wasu gungun jama’a ke bijirewa, wasu ke neman canji ko da gora, wasu ke ganin cewa bin matakin yin adawa, addini ne, ba kuma za su daina ba. A wannan lokaci wanda aka danne bai damu da ya tunkari tankunan yaki ba, in dai hakan ne kurum zai sa ya kasance da ba bawa ba a cikin kasarsa.

Za mu ci gaba