Nazari: Mawaki Rarara da yankan kunkurun Bala (5)

A cikin jaridar Daily Comet, musamman a shafukanta na Hausa, aka shiga fallasa da yin zage-zage game da ayyukan assha na gwamnatin ’yan mulkin mallaka da hukumomin En’e-En’e da lalatattun manofofin jam’iyyar NPC, musamman lokacin da zabe ya kusa a shekarar 1956. ’Yan NEPU sun yi amfani da wannan dama wajen mayar da zagi da […]

Nazari: Mawaki Rarara da yankan kunkurun Bala (5)
Nazari: Mawaki Rarara da yankan kunkurun Bala (5)

A cikin jaridar Daily Comet, musamman a shafukanta na Hausa, aka shiga fallasa da yin zage-zage game da ayyukan assha na gwamnatin ’yan mulkin mallaka da hukumomin En’e-En’e da lalatattun manofofin jam’iyyar NPC, musamman lokacin da zabe ya kusa a shekarar 1956. ’Yan NEPU sun yi amfani da wannan dama wajen mayar da zagi da fallasar NPC, suka shiga yayata da daga jam’iyyar NEPU da manufofinta. A wannan lokaci ba wai magana ce ta fadar gaskiya ba, harka ce ta farfaganda, neman suna da nuna iya adawa. Wannan shi ya kara haifar da rarrabuwa da jan daga a tsakanin jam’iyyun biyu, adawa da koma “yaki” kunya ta kau sai tsageranci ya zama abin ado ba wai manufofin jam’iyyun ba. Wannan shi ya haifar har ta kai ana zagi karara ga shugabanni da masu goya wa jam’iyyun baya da kuma lalata manufofin jam’iyyun da gwarzayen da ake ji da su ko wadanda ake jin cewa su ne wuka, su ne nama a lokacin zabe ko yakin neman kuri’a.
Daga wannan lokacin sai abubuwa suka sake rincabewa, kamfen ko yakin neman zabe na sanin ya kamata da amfani da manufofin jam’iyya ya kau ko aka yi watsi da shi, musamman ma a wajen ’yan NEPU da suka sha zagi da tsinuwa da dauri da kisa na wani lokaci mai tsawo, kuma aka hana su su koka. Saboda haka duk bayanin da ya fito daga wajen ’yan NEPU, a wajen yakin neman zabe ne, ko a ckin jaridu ne ko a wake ne, za a iske shi cike yake da zagi da zambo za habaici da zambo-zagi. Shi ya sa jagororin jam’iyyun biyu suka shiga uku a tsakanin magoya baya, Aminu Kano da Sa’adu Zungur (a NEPU), sai kuma Sardauna, Tafawa balewa da Sarkin Kano (a NPC).
’Yan jam’iyyar NEPU dai an dauke su a matsayin jakai, Malam Aminu Kano cewa suka yi bai kamata a ce yana shugabantar jama’a ba tun da wai ba a yi masa kaciya ba. Ita kuwa jam’iyyar NPC, jam’iyya ce ta masu yin ludu, Sarkin Kano an yi masa lakabi da “dan makahon birni.” Manyan magoya bayan jam’iyyar NPC, musamman a Kano an ce “ba sa yin amfani da matansu na sunna” da sauransu.
Haka kuma wasikun da ake aiko wa Editocin wadanan jaridu na Sodangi da Daily Mail da Daily Comet, ba ruwansu da bin ka’idojin aikin jarida na boye zagi ko kin bata suna ga wani. A cikin wasikun za ka ji an kira abokin adawa “jahili” ko “wawa,” manyan malamai a kira su da “banzan-bazara,” shi kuwa talaka ko gyartai ya zama “mai gari.”
Misalan da za mu iya badawa a nan su dace da aukuwar wannan tashin-tashina su ne daga rubuce-rubucen danjani Hadeja. A duk inda danjani ya yi rubutu a cikin Daily Comet (bangaren Hausa) to ka tabbata ya yi haka ne domin ya wanke jam’iyyar NEPU daga zargin NPC, ya nuna cewa NEPU jam’iyya ce ta Musulunci, jam’iyyar NPC ita ce ta kafirai, yana yi, yana kafa hujjoji da Alkur’ani da Hadisai. Ya taba rubuta irin wannan zance a cikin jaridar Daily Comet domin mayar da martani ga ’yan NPC:
“Kai wawa, jahili, dakiki, sususu, bari in gaya maka duk cikin Shari’ar Islama ba inda aka ce a nuna bambanci, ba inda aka ce a bada kudi don neman galaba, ba inda aka ce a girmama Sardauna a wulakanta Gyartai. In kuwa akwai, ka gaya mani ayar da ta ce a yi kukan masallaci na karya don jin dadin Sardauna da jam’iyyarsa. Kuma wace aya ce ta ce wasu sarakuna su sayi motoci da kudin talakawa? Wace aya ce ta ce shugabanni su dinga luwadi?”
Siyasar tashin tashina, irin wannan ta samo asali ne daga irin dangantakar da ke tsakanin gwamnatin mulkin mallaka da hukumomin En’e-En’e da sarakuna da ’yan tagajan gari. Shi yaki ko tshin-tashina irin ta siyasa, ba ta raggo ko matsoraci ba ce, don haka abin da ’yan NEPU ke takama da shi bai wuce cewar nan ba ta “an ga kabarin mai kuru amma ba a ga na matsoraci ba.” Shi ya sa ’yan NEPU ba su ji tsoron rama cuta ga macuci ba, ba su ja da baya ba. Duk inda aka ce Alkur’ani ya ce kaza game da NPC, ’yan NEPU za su ce ba haka ba ne ta amfani da tawilinsu. Ga wani misali, a wani jawabi da wani Malam Usuman Shehu ya yi a jaridar Sodangi ta ran 6/4/60, ya kawo hujjoji da ke nuni da cewa ’yan NEPU ba Musulmi ba ne, domin ba sa yin da’a ga shugabanninsu kamar yadda Allah Ya umurta a cikin Alkur’ani. A ra’ayin danjani Hadeja, sai ya ga cewa akwai rashin tunani da rashin fahimtar addini ga wannan bayani, domin haka sai ya mayar da mantani yana cewa:
Wurin da ka ce “bin na gaba…,” wannan aya ce ba su ne suka saukar da ita ba. Ko Malam Shehu bai san na gaban da Allah yake nufi ba ne? Su wadanda Allah ya ce a bi su, suna gaban wadanda za su yi umarni ga kyakkyawan aiki, su yi hani ga barin mummunan aiki, ba cewa aka yi a bi Sarki, Koguna ko Sardauna kurum ba. Sai in za su yi umarni a bi dukkan abin da Allah ya ce a yi. Ko kana nufin mu bi malamai, su bi Sarki da Sardauna, su kuma Sarki da Sardauna su bi Turawa?”
Ba a wasiku da bayanan jarida ake samun irin wadannan bayanai na siyasar Yankan Kunkuna Bala ba, an sami haka a wake-waken siyasar wancan zamani. Idan bayanan da ake yi a jaridu daga masu ilmin boko ne da wayewar kan zamani, to su mawakan yawancinsu ba su yi karatun boko ba, sun dai sami ilminsu a makarauntun addini da kuma makarantar Malam Aminu Kano da wasu irinsa. Ire-iren abubuwan da suka koya daga makarantun allo, wasu kuma daga wajen Malam Aminu Kano da mukarrabansa, su ne suka amayar ta hanyar rubuce-rubucen wakokin siyasa. Sai dai a wancan lokaci a maimakon turaku biyu da aka saba da su, wato na magoya bayan NPC da NEPU, an kuma sami wadansu da za a iya kira da “’yan ba-ruwanmu” kodayake su ma daga cikin gyauron NPC suka fito. Ire-iren wadannan mawaka ba su amince da siyasar tashin-tashina da cin mutunci ba ta haryar waka. Kamar yadda Alkali Bello Gidadawa ya bayyana, ya ce, shi a nasa tunanin, siyasa ba abin a mutu ko a yi rai ba ce, abin ra’ayi ce ko kuma kare ra’ayin cikin halayya ta gari.
Za mu karkare makon gobe