Real Madrid ta fitar da Man City a Gasar Zakarun Turai

Mbappe ya yi wa Manchester City kaca-kaca ta hanyar zura mata ƙwallaye uku rigis a raga.

Real Madrid ta fitar da Man City a Gasar Zakarun Turai

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid ta sake doke Manchester City da ci 3 da 1 a filin wasa na Bernabeu.

Madrid ta karɓi baƙuncin Man City a wasan zagaye na biyu na gasar Zakarun Turai, bayan doke ta a gida da ci 3 da 2.

Kylian Mbappe ne ya zama tauraro a wannan wasan, inda ya jefa wa Manchester City ƙwallaye uku rigis a raga.

Ɗan wasan gaban na Real Madrid, ya fara jefa ƙwallo ta farko a minti na 4 da fara wasa, sannan ya jefa ƙwallo ta biyu a minti na 33.

Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci ne, Mbappe ya sake jefa ƙwallo ta uku a ragar Manchester City a minti 61.

A minti na 92 ɗan wasan Manchester City, Nico Gonzalez, ya warware mata ƙwallo ɗaya.

A haka wasan ya ƙare, amma Jude Bellingham ya samu katin gargaɗi, wanda hakan ke nufin ba zai buga wa Madrid wasanta na gaba a gasar ba.

Idan aka raba jadawalin ƙungiyoyin da za su kara da juna, Real Madrid za ta iya haɗuwa da Bayer Leverkusen ko Atletico Madrid.