Ruwan markadadden kwado magani ne a Peru

Saboda matsalolin da suka hada da dugunzuma cikin damuwa da ciwon jiki da rashin karfin namiji, da ake fama da su a yankin tsaunukan Andean da ke kasar Peru, mazaunan karkara a yankunan sun yi amanna da cewa shan rowan markadadden kwado babban magani ne.Sai dai rashin sa’ar da mutanen kasar Peru suka yi har […]

Ruwan markadadden kwado magani ne a Peru
Ruwan markadadden kwado magani ne a Peru

Saboda matsalolin da suka hada da dugunzuma cikin damuwa da ciwon jiki da rashin karfin namiji, da ake fama da su a yankin tsaunukan Andean da ke kasar Peru, mazaunan karkara a yankunan sun yi amanna da cewa shan rowan markadadden kwado babban magani ne.
Sai dai rashin sa’ar da mutanen kasar Peru suka yi har yanzu babu sakamakon wnai bincike na kimiyya day a yi nuni da cewa shan lemun markadadden kwado na warkar da cututtuka. Mafi yawan kwadin da suke markadawa, nau’uka ne na Telmatobius Culeus, kamar yadda aka fassara su a Turancin kimiyya, sannan ana kamo su ne a cikin tafkin Titicaca, wani wuri da Cibiyar Kare Muhalli ta Duniya ta tabbatar da cewa yana tattare da hadari.
Kwado sukutum ake markadawa a cikin na’urar markade, don maganin cututtukan da suka hada da sarkakiyar numfashi ko toshewar huhu da rashin karfin jiki da rashin karfin namiji.
Wata mai sarrafa lemun markadadden kwado, Maria Cruz ta kan makure kwado har sai ya mutu, snanan ta fere fatarsa, sai ta jefa shi cikin na’urar markade (blender), t ahada da jijiyar karas din maca da ake nomawa a kasar Peru, ta kuma cakuda shi da zuma.
Wannan markade yakan fito da ruwa mai launin kore. Ita kuwa Cruz sai ta zuba a modar tangara tana raba wa wadanda suka zo ciniki rumfarta.
“Markadadden kwado na maganin sankarar jinni da toshewar huhu da ciwon kashi da rudani da damuwa, kuma kananan yara da manyan mutane da ke fama da cututtukan sarkakiyar numfashi har ma da tarin fuka, su ke zuwa wajenta,” kamar yadda Cruz ta yi ikrari.
daya daga cikin masu sayen wannan markade, Cecilia Cahuarra, ’yar shekara 35, ta yi amanna da wannan magani.
“Ina zuwa nan kusan kodayaushe don shan lemun markadadden kwado, saboda yana da alfanu ga yara da masu cutar sankarar jini da toshewar huhu, har ma da tsofaffin mutane suna samu matukar fa’ida a tattare da shi,” inji ta.
Shi kuwa Dokta Tomy billanueba, Shugaban Kwalejin Koyon Aikin Likitanci da ke Lima, ya ce: babu wani bincike na kimiyya da hujjarsa ta tabbatar da cewa markadadden kwado na maganin kowace irin cuta, sai dai kawai wannan wata al’ada ce ta mutanen Andean.”