Saurayi da budurwarsa sun sace kayan lefen ’yar uwarsa a Kano

Budurwar ta shaida wa kotu cewa biyu daga cikin kayan lefen da aka sace saurayin ya kawo mata

Saurayi da budurwarsa sun sace kayan lefen ’yar uwarsa a Kano

Gidan yari

Kotun Musulunci ta tsare wata budurwa da saurayinta a gidan yari kan zargin sace kayan lefen ’yar uwarsa.

An gurfanar da saurayin da budurwarsa ne a kan zargin sata da kuma karbar kayan sata a gaban Kotun Musulunci da ke zamanta a unguwar Rijiyar Lemo a Jihar Kano.

Bayan jami’i mai gabatar da kara, Usman Idris Shu’aibu Dala, ya karanto takardar tuhumar, saurayin ya amsa laifinda ake zargin sa.

Amma ita budurwar ta shaida wa alkali cewa biyu daga cikin kayan lefen da ake zargi kawai saurayin nata ya kawo mata, kuma ta mika su ga kotu.

Bayan sauraren su, alkalin kotun, Khadi Danbaba, ya ba da umarnin tsare su a gidan yari zuwa ranar Larabar nan.

Ya kuma ba da umarnin zuwa da iyayensu a zaman kotun da za a ci gaba ranar Laraba.