Shekara 50 ina cin mushen da mota ta kade -Boyt

Wani mutumin Birtaniya, tsoho dan shekara 74, ya bayyana cewa ya shafe shekara 50 yana cin mushen dabbar da aka kade a titi, kuma babu naman da ya fi shi dadin ci. Mutumin mai suna Arthur Boyt ya damfaru da wannan dabi’a ta son cin mushen da aka kade a titi tun a shekarun 1960, […]

Shekara 50 ina cin mushen da mota ta kade -Boyt

 Authur Boyt rike da mushen magen da aka kasheWani mutumin Birtaniya, tsoho dan shekara 74, ya bayyana cewa ya shafe shekara 50 yana cin mushen dabbar da aka kade a titi, kuma babu naman da ya fi shi dadin ci. Mutumin mai suna Arthur Boyt ya damfaru da wannan dabi’a ta son cin mushen da aka kade a titi tun a shekarun 1960, kuma yana ganin kamata ya yi a ce sauran mutane sun fara aikata irin dabi’arsa.
“Mutane kan ce kaico,’ a duk sa’adda na furta cewa ina naman dabbar da aka kade a titi, ni kuwa sai in ce idan kuka dandana, akwai yiwuwar ku ji dadinsa,” a cewar Boyt, kamar yadda ya bayyana wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP, a daidai lokacin da tukunyar miyar romon namansa ke zababbaka a tukunya.
“Ba wai dandanon abincin ba ne, abin a cikin kai yake. Da kakai makura wajen cin irin wannan naman, to za ka tabbatar hakika nama ne mai kyau,” inji shi.
Boyt kwararren mai bincike ne, don haka ya bayyana cewa naman kare ya fi so, ya fi cin nau’ukan karnuka da ake yi wa lakabi da Lurchers da Labrador, wadanda mota ta kade. Ya kuma ce yakan yi kokarin neman masu dabbobi kafin ya cinye su.
Ya ce bai da mu da rubewar nama ba, ballantan warinsa. Domin idna ka girka shi da kyau, rubewarsa bai zai hana mutum jin dadin naman dabbar ba; ko da ta mutu da makonni biyu, har tsutsotsi sun fito a jikinta.
“Naman mushen da aka kade a titi bai taba sanya ni rashin lafiya ba. Mutanen da suka ci abincin rana a nan, sun yi fama da rashin lafiya da zarar sun koma gida, amma ina ganin wannan wani al’amari ne daban,” a cewarsa.
Cin mushen dabbar da aka kade a titi, doka ta amince da hakan a Ingila, matukar hadari ne, kuma ba da gangan aka kashe dabbar ba.
Boyt ya bayyana cewa yana cin naman dabbar da aka kade bisa kuskure ne kawai, idan ya samu naman da kansa, ko kuma makwafta suka sanar da shi cewa a kusa da dajin Bodmin Moor, inda ake farauta an ga mushen magen dawa. Kuma yana girka irin wannan naman ne da zarar matarsa ba ta gida, domin ita ba ta cin nama sai ganyayyaki.
“Ta kana ziyarci mahaifiyarta sau daya a mako, don haka idan ta yi dare, irin wannan lokaci dama ta samu ta kwasar lagwada,” inji shi. Boyt na kwasar lagwada tare da kwankwadar giyar mutanen Arewacin kasar Spain ta Rioja.

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan