Sojoji Sun Kashe ’Yan Boko Haram 23 A Borno

Sojojin sun ragargaji mayaƙan ƙungiyar a yankin Malam Fatori

Sojoji Sun Kashe ’Yan Boko Haram 23 A Borno

Dakarun sashe na 3 na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Ƙasa da Ƙasa (MNJTF) sun yi nasarar kashe  ’yan ta’addan Boko Haram 23 a Jihar Borno.

Fafatawar ta faru ne a ranar Lahadi, 23 ga watan Satumba, a kusa da Malam Fatori, bayan wata arangama inda sojoji suka dakile wani harin da maharan suka kai musu.

A cewar masanin harkokin tsaron nan a tafkin Chadi Zagazola Makama, sojojin sun yi wa mayakan na ISWAP kwanton bauna, inda suka yi ta harbe-harbe da ya yi sanadin mutuwar ’yan ta’adda 23 wasu da yawa kuma suka tsira da munanan raunuka.

A cewarsa, a yayin fafatawar  wasu sojojin Najeriya biyu suka samu raunuka, amma ba a samu asarar rai ba a cikin sojojin.

Haka nan dakarun na MNJTF sun kwato makamai masu yawa daga hannun ’yan ta’addan da suka haɗa da bindiga kirar PKM, bindiga AK-47, gurneti da harsasai masu tarin yawa.

Mutum 10 sun mutu a wajen rabon tallafin abinci a Abuja

Tirela murƙushe ’yan sanda 3 har lahira

An ƙwace kwantainoni 54 mallakin Emefiele

Fulawa da dabbobin Fadar Shugaban Ƙasa za su ci N125m a 2025