Sunan Muhammad ne aka fi son sanya wa jarirai a Birtaniya

Muhammad ya zama mashahurin sunan da aka sanya wa jarirai maza a kasar Birtaniya, kamar yadda cibiyar kula da raino da masu juna biyu, ta tabbatar a shafin sadarwarta na BabyCentre. Wannan kuwa ya biyo bayan wani binciken da shafin sadarwar rainon ’ya’ya na BabyCentre ya gudanar, amma ba shi ne hakikanin alkaluman kidayar kasa […]

Sunan Muhammad ne aka fi son sanya wa jarirai a Birtaniya
Sunan Muhammad ne aka fi son sanya wa jarirai a Birtaniya

Muhammad ya zama mashahurin sunan da aka sanya wa jarirai maza a kasar Birtaniya, kamar yadda cibiyar kula da raino da masu juna biyu, ta tabbatar a shafin sadarwarta na BabyCentre.

Wannan kuwa ya biyo bayan wani binciken da shafin sadarwar rainon ’ya’ya na BabyCentre ya gudanar, amma ba shi ne hakikanin alkaluman kidayar kasa ba.
Sunan Muhammad ya shiga gaban Jack da Oliber, inda ya kara kimar daraja daga na 27 a bara zuwa na farko a jerin sunaye 100 da aka fitar na shekarar 2014. Sunan Larabawa da suka hada da Omar da Ali da Ibrahim sun samu shiga jerin farko na wannan rukunin sunaye a bana.
Sarah Redshaw, Babbar Editar shafin BabyCentre, ta bayyana wa jaridar The Guardian cewa: “Yawan sunanyen Larabawa da na Aarab, wato yaran Indiyawa a cikin jerin sunaye 100 na nunin da karin bambance-bambancen jinsi da ake samu a kasr Birtaniya a yau.”
Muhammad sunan Musulunci ne na Ananbin da aka fi girmamawa, wanda ma’anarsa ke nufin “Godiya ga Allah” da “Abin godewa” a cikin harshen Larabci. An fara ganin sunan Muhammad a jerin sunaye mafi shahara tun a shekarun 1950, sai ga shi Muhammad ya shiga gaban kowane suna a shekarar 2014. A kan furta wannan suna da salo-salo har sau 10, wadanda aka tattara ywwansu har ya kai ga zama suna mafi shahara a jerin alkaluman kididdigar binciken da shafin sadarwar BabyCentre ya gudanar.
A jerin sunayen mat akuwa, Nur ta kasance suna na 29, inda darajar sunan Maryam ya daga daga na 59 zuwa na 35 a bana.
Sannan an samu raguwar sunayen ’yan gidan sarautar Birtaniya a wannan shekarar, ind asunayen da suka hada Charlie da Harry suka yiwo kasa da daraja uku, kownaensu, ind asuka zama na shida d ana bakwai a jerin sunayen; sannan William ya fado kasa da daraja 12. Shi ma sunan George ya sulmiyo kasa da daraja biyar, zuwa suna mai kimar daraja ta 18.