Tsakanin ilimi da kudi, wanne ya fi wahalar nema?3
Yau filin muhawara ya kawo tambayar ko tsakanin ilimi da kudi wanne ya fi wahalar nema, kuma mutanen da aka tuntuba sun bayar da gudunmawarsu ne kamar haka: Kudi ya fi wahalar nema -Maryam Jibrin BirgedA ra’ayina kudi ya fi ilimi wahalar nema, saboda a yanzu sai mutum yana da kudi zai sami ilimi. ’Ya’yan […]
Yau filin muhawara ya kawo tambayar ko tsakanin ilimi da kudi wanne ya fi wahalar nema, kuma mutanen da aka tuntuba sun bayar da gudunmawarsu ne kamar haka:
Kudi ya fi wahalar nema -Maryam Jibrin Birged
A ra’ayina kudi ya fi ilimi wahalar nema, saboda a yanzu sai mutum yana da kudi zai sami ilimi. ’Ya’yan talakawa nawa ne a yanzu ke son yin karatu, amma abin ya gagare su saboda rashin kudi? Idan mutum yana da kudi, zai iya shiga kowace irin makaranta a duniya ya samu ilimi. Don haka kudi ya fi wahalar nema, duk da cewa shi ma ilimin yana da tasa wahalar kafin a same shi.