Tsoron fushin matata ya sa na bar sigari -Obama

Shugaban kasar Amurka Barack Obama ya yi ikrarin barin zukar taba saboda tsoron fushin matarsa, kamar yadda wani amsa kuwa ya zuko maganarsa da yake yi da wani mutum a wani gefe, lokacin taron Majalisar dinkin Duniya.Shugaban Amurka, wanda ya tattauna a gefe kan muhimancin kungiyar fafutikar hakkin dan Adam, a ranar Litinin din da […]

Tsoron fushin matata ya sa na bar sigari -Obama

Shugaba Barack Obama da uwargidansa MichelleShugaban kasar Amurka Barack Obama ya yi ikrarin barin zukar taba saboda tsoron fushin matarsa, kamar yadda wani amsa kuwa ya zuko maganarsa da yake yi da wani mutum a wani gefe, lokacin taron Majalisar dinkin Duniya.
Shugaban Amurka, wanda ya tattauna a gefe kan muhimancin kungiyar fafutikar hakkin dan Adam, a ranar Litinin din da ta gabata, sai ya koma gefe don yin wasu maganganu na daban. Ana cikin haka sai Gidan Talabijin na CNN ya zuko hoton Obama a gefe yana tambayar wani mutum ko ya daina shan taba? Da mutumin ya dawo masa da irin wannan tambayar, sai cikin fara’a da annashuwa ya ce: “Ina jin cewa na daina zukar taba  a tsawon shekara shida. Wannan kuwa duk saboda tsoron fushin matata ne.”
Obama dai mutum ne mai kokarin kula da lafiyar kansa, amma ya damfaru da shan taba, har ma ta kai ga yana siffanta kansa, a matsayin matashin da ya tashi yana shan taba, kamar yadda yake kunshe a cikin litafin da ya wallafa, mai taken “Burin mahaifina (Dreams from My father, a Turanci).”
Yawan shan tabar Obama sai da ya zama abin magana a lokacin da yake yakin neman zabe, a fafutikarsa ta shiga Fadar White House, a shekarar 2008.
A shekarar farko da ya kama ragamar mulki, Obama ya bayyana kansa a mtsayin wanda ya warke daga cutar shan taba da kimnanin “kashi 95 cikin 100,”  sai dai ya yi ikrarin cewa yak an dan zuka da lokaci zuwa lokaci, a kokarinsa na barin shan tabar.
A shekarar 2010, Mai magana da yawun fadar White House, Rober Gibbs ya bayyana cewa Obama ya shafe watanni tara bai zuki taba ba, amma ya yi  matukar fafutika, duk da nauyin shugabanci da ya rataya a kansa.
Uwargidan Shugaban kasa, Michelle Obama, wadda ta shahara wajen fafutikar kula da lafiyar al’umma, ta sha nuna takaicinta a fili kan yadda mijinta ke shan taba, amma sai dai a cewarta ba ya kunna wutar taba a gaban ’ya’yansu biyu.
A cikin watan Fabrairun 2011, ta ce mijinta ya shafe shekara bai sha taba ba, don haka ba ta matsa masa kan wannan matsalar.
“Idan mutum yana yin aikin kwarai, to bai kamata a dagula masa lissafi ba,” injita.

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan