Wani kauyen Indiya ya hana ’yan mata sanya wandon jeans da rike wayar salula

Wani kauye Phulwaria da ke Arewacin Bihar, Jihar da ke Gabashin kasar Indiya, ya fito da dokar hana mata sanya wandon jeans da amfani da wayar salula, musmaman wadanda ke zuwa makarantu da kwaleji. Wannan kauye dai yana karkashin wani mashahurin dan siyasa Cif Lalu Prasad da jam’iyyarsa ta Rashtriya Janata Dal (RJD).Wannan hukunci da […]

Wani kauyen Indiya ya hana ’yan mata sanya wandon jeans da rike wayar salula
Wani kauyen Indiya ya hana ’yan mata sanya wandon jeans da rike wayar salula

Wani kauye Phulwaria da ke Arewacin Bihar, Jihar da ke Gabashin kasar Indiya, ya fito da dokar hana mata sanya wandon jeans da amfani da wayar salula, musmaman wadanda ke zuwa makarantu da kwaleji. Wannan kauye dai yana karkashin wani mashahurin dan siyasa Cif Lalu Prasad da jam’iyyarsa ta Rashtriya Janata Dal (RJD).
Wannan hukunci da doka sun fara aiki nan take, bayan da majalisar mulkin ta gudanar da taronta, a karkashin shugaba Sabitri Debi, tare da goyon bayan shugaban sashen shari’a, Asmina Khatoon. Kuma taron ya samu hlartar wakilai daga daukacin kauyukan da ke karkashin majalisar.
Rahotanni sun nuna cewa, taron ya nuna takaicinsa kan yadda ake smaun karuwar keta haddi da lalata da fyade, al’amuran da aka dora alhakin aukuwarsa kan yadda ’yan mata suka ari tsarin rayuwar Yammacin Turai suka yafa, a tsarin sanya sutura da kuma amfani da wayar hannu.
Taron ya yanke matsaya wajen yin fadakarwa ga daukacin al’umma don tabbatar da cewa kowa ya bi dokar. Sannan mahalartar sun roki iyaye da masu rikon ’ya’ya da kada su saya wa ’ya’yansu mata wanduna jeans da wayoyin salula, saboda a cewarsu, su tushen duk wasu musifu da ke cutar da al’umma.
“Tun daga yanzu, mun gano munanan abubuwa da ke gurbata ’yan mata, al’amuran da suka hada da amfani da wayar salula da yawan koyin da al’adun Yammacin Turai. Za kuma mu shawo kan matsalolin ne ta hanyar dakile amfani da wadannan kayayyaki ga ’yan mata da ke makarantu da kwaleji,” a cewar Shugaban Majalisar mulkin kauyen, Sabitri Debi, kamar yadda ya bayyana wa manema a ranar Talatar da ta gabata. Ta ce, tun daga yanzu ba za a kyale ’yan matan da ke sanye da jeans ko suke rike da wayar salula shiga aji ba.
Sannan ta yi barazanar daukar mataki a kan ’yan matan da suka ki bin wannan doka. “’Yan matan da suka keta wannan doka, ba korarsu kawai za a yi daga makaranta ba, har ma za su rasa duk wnai tallafin gwamnati,” kamar yadda shugabar kauyen ta yi gargadi.
A makon da ya gabata ma an samu kauyen a gundumar Gopalganj  da ya hana mata ‘makaranta sanya wandunan jeans da wayoyin salula.