Yahudawa sun samu izinin aiki a kasar Saudiyya

Bakin kasashen waje da ke bin tafarkin addinin Yahudanci sun samu izinin yin aiki a kasar Saudiyya, kamar yadda wata majiya daga ma’aikatar kwadago ta bayyana.“Ma’aikatar bat a damu  da bayar da izinin aiki ga Yahudawka ba, tunda tana hulda mutanen kasashe daban-daban, amma ba mabiya addinai daban-daban,” kamar yadda majiyar ta bayyana wa jaridar […]

Yahudawa sun samu izinin aiki a kasar Saudiyya
Yahudawa sun samu izinin aiki a kasar Saudiyya

Bakin kasashen waje da ke bin tafarkin addinin Yahudanci sun samu izinin yin aiki a kasar Saudiyya, kamar yadda wata majiya daga ma’aikatar kwadago ta bayyana.
“Ma’aikatar bat a damu  da bayar da izinin aiki ga Yahudawka ba, tunda tana hulda mutanen kasashe daban-daban, amma ba mabiya addinai daban-daban,” kamar yadda majiyar ta bayyana wa jaridar Al-Watan.
Saudiyya ba ta adawa da hulda da wani addini, kuma Cibiyar Tatttaunawa da Addinai da Al’adun duniya ta Sarki Abdullah Bin Abdul Aziz shaida ce kan hakan,” inji majiayar.
Wannan cibiya dai an kafa ta ne a babban birnin kasar Austria da ke bienna, sannan an samar da ita ne don karfafa tattaunawa a tsakanin mabiya addinai da al’adu da ke fadin duniya. Sannan an tabbatar da cewa: “kungiyar Duniya ce mai cin gashin kanta, wadda babu wani ra’ayi na siyasa ko tsarin tattalin arziki da ke da tasiri a kanta.”
“Alal misali, idan mutum dan asalin kasar Yemen ne, kuma mabiyin addinin Yahudanci, za a iya bas hi izin yin aikin a masarautar, tunda ma’aikatar ba ta la’akari da addinai, amma tana yin dubi ne ga kasashe,” a cewar majiyar.
Shafin sadarwar ma’aikatar ya jero sunan addinin Yahudanci a daya daga cikin addinai 10, wadanda mabiyansu za su iya neman aiki a kasar.
Wani dan majalisar Shur, Sadaka Bin Yahjya Fadhel, ya ce ma’aiktar kwadago ta yi daidai da ta bai wa Yahudawa izinin zama ma’aikata.
“Mu Musulmi ba mu da wata matsala da Yahudanci ko Kiristanci, amma matsalarmu it ace akidar kungiyar Yahudawa ta Sahayoniya (Zionism), wadda ke amfani da addinin don yada manufofinta,” inji shi.
Ya yi karin haske game da bambanci da ke tsakanin Yahudanci da Sahayoniyanci:
“Za mu iya yin hulda da kowane mutum da ke bin kowane irin addini, don haka mna’aikatar ta yi daidai, tunda ba da kasar Isra’ila take yin hulda ba. A matsayin kasar na masarauta, muna maraba da daukacin addinai, amma ba za mu iya yin hulda da Isra’ila ba. Saboda suna da alaka da Sahayoniyanci, a matsayin kungiyar ’yan mulkin mallaka, da ke fakewa da addinin Yahudanci. Addinin Yahudanci ba shi da wata alaka da wnanan kungiya,” a cewarsa kamar yadda ya bayyana wa wata jaridar kullum ta kasar Saudiyya.