’Yan bindiga sun kashe limami a masallaci a Abuja

’Yan bindiga sun harbe wani limami har lahira a masallaci sannan suka yi awon gaba da mutum ɗaya a birnin Abuja.

’Yan bindiga sun kashe limami a masallaci a Abuja

’Yan bindiga sun harbe wani limami har lahira a masallaci sannan suka yi awon gaba da mutum ɗaya a birnin Abuja.

Maharan sun kuma yi awon gaba da wani shahararren mai harka sufuri, Alhaji Salisu Danfulani a lokacin harin na ranar Lahadi da dare.

Sun kai harin ne a daidai lokacin da jama’a suke fitowa daga masallaci bayan kammala Sallar Isha a gareki ’yan tifa da ke yankin Mpape.

Wani mazaunin unguwar Mpape, Nasiru Ahmad, ya ce limamin masallacin, mai suna Malam Ahmad Maidara ya yi ƙoƙarin tserewa, amma aka yi rashin sa’a wasu daga cikin ’yan bindigar sun riga sun tare hanyar da ya bi, inda suka harbe shi nan take ya ce ga garinku nan.

Ya ce maharan sun kuma harbi wani mutum guda a hannu, amma an kai shi asibiti domin ba shi kulawa.

Rahotanni sun nuna cewa ’yan bindigar sun ɓullo ne ta wani tsauni da ke makwabtaka da yankin, kuma ta nan suka koma.

Shugaban Ƙungiyar Ma’aikata Masu Haƙar Ma’adinai ta Najeriya, (NUMW), Kwamred Hamza Muhammad, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce an kai gawar Malam Ahmad Maidara gidansa da ke garin Gwagwa inda aka yi kasa jana’iza a ranar Litinin.

Mutum 10 sun mutu a wajen rabon tallafin abinci a Abuja

Tirela murƙushe ’yan sanda 3 har lahira

An ƙwace kwantainoni 54 mallakin Emefiele

Fulawa da dabbobin Fadar Shugaban Ƙasa za su ci N125m a 2025