’Yan rawa sun caccaki limaman addinin Buddha a Myanmar kan adawa da Musulmi

Jagaban ’yan rawa na kasar Myanmar Mista Kyaw Kyaw, ya jagoranci ’yan tawagarsa, wadanda suka ruguje da kida da waka suna caccakar limaman addinin Buddha a titunan birnin Yangon, kan adawarsu ga Musulmi, wadda ke yawan haifar da tashe-tashen hankula a kasar.Wadannan matasa ’yan rawa da waka sun kai su 20, inda suka yi magana […]

’Yan rawa sun caccaki limaman addinin Buddha a Myanmar kan adawa da Musulmi

Kyaw Kyaw, jagoran masu adawa da limaman addinin Buddha a MyanmarJagaban ’yan rawa na kasar Myanmar Mista Kyaw Kyaw, ya jagoranci ’yan tawagarsa, wadanda suka ruguje da kida da waka suna caccakar limaman addinin Buddha a titunan birnin Yangon, kan adawarsu ga Musulmi, wadda ke yawan haifar da tashe-tashen hankula a kasar.
Wadannan matasa ’yan rawa da waka sun kai su 20, inda suka yi magana kan wannan matsala da ta addabi kasarsu, alhali kowa ya yi shiru a kan lamarin.
“Idan su limaman addini ne na gaskiya da na shiru, amma ba su ba ne ba,” in ji Mista Kyaw Kyaw, jagoran makada da mawakan matsa, wadanda suka la’anci munafuncin addini da nuna kiya yya ga Musulmi.
Wannan kungiya ta matasan masu raye-raye da wake-wake sun yi mata lakabi da lambar “969.”
“Masu kishin kasa ne, da akidar kama-karya. Babu wanda ke son jin wanan, amma gaskiya ce,” inji shi.
Limaman addinin Buddha masu tsattsauran ra’ayi su ne gaba-gaba wajen nuna kiyayya ga Musulmi, wadand suka kasance ’yar tsiraru a wannan kasa mai yawan al’umma mutum miliyan 60, kuma babu wanda ke iya yin maganar nuna aibin masu wannan mummunar akida.

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan