‘Yan sama-jannati sun shafe kwana 371 a sararin samaniya

An shirya za su dawo duniya a ranar 28 ga watan Maris, 2023, amma hakan bai yiwu ba.

‘Yan sama-jannati sun shafe kwana 371 a sararin samaniya

Dan sama-jannati Frank Rubio a hannun
ma’ikatan da suka gano jirgin da ya sauko da shi daga sararin samaniya inda ya shekara.

Wasu ’yan sama-jannati sun dawo duniyarmu bayan sun yi kwanaki ɗaiɗai har 371 suna shawagi a sararin samaniya wanda hakan ya sa suka zama mutane na farko a duniya da suka taba yin haka a tarihi.

Frank Rubio dan kasar Amurka an harba shi zuwa sararin samaniya domin aikin gwaje-gwaje da bincike a tashar kasa-da-kasa (ISS) da ke sararin samaniya.

An yi hakan ne a karkashin Hukumar NASA mai bincike kan sararin samaniya, tare da ’yan kasar Rasha biyu, Sergei Prokopyev da Dmitri Petelin a ranar 21 ga Satumban bara.

An shirya za su dawo duniya a ranar 28 ga watan Maris, 2023, amma hakan bai yiwu ba, saboda haɗari da kumbon da ya kai su ya yi a lokacin da suke shirin dawowa a dalilin taho-mu-gama da wani dutse a samaniya, a watan Disamban 2022.

An dawo da kumbon nan duniya aka gyara, sannan aka sake aikawa da shi Tashar ISS inda Frank da sauran abokan aikinsa suke, kuma suka shiga ya dawo da su duniyar a ranar 27 ga Satumban da ya gabata.

A cewar jaridar labaran kimiyya ta Live science, Rubio shi da sauran ’yan sama-jannati Sergey da Dmitri sun dawo lafiya.