’Yar autar Ahmadou Ahidjo ta shiga jam’iyyar Paul Biya

Yar autar tsohon Shugaban kasar Kamaru Ahmadou Ahidjo, Aminatou Ahidjo  ta dawo kasar bayan ta shekaru 30 tana gudun hijira a kasar Senegal, tare da mahaifiyarta Habiba da sauran ‘yan uwanta. A karshen watan Agusta ta dawo gida ta fara kusantar jam’iyyar RDPC, ta Shugaban Paul Biya, inda ta nuna cewa tsarin siyasar da yake […]

’Yar autar Ahmadou Ahidjo ta shiga jam’iyyar Paul Biya

Aminatou Ahidjo, autar Ahmadou AhidjoYar autar tsohon Shugaban kasar Kamaru Ahmadou Ahidjo, Aminatou Ahidjo  ta dawo kasar bayan ta shekaru 30 tana gudun hijira a kasar Senegal, tare da mahaifiyarta Habiba da sauran ‘yan uwanta. A karshen watan Agusta ta dawo gida ta fara kusantar jam’iyyar RDPC, ta Shugaban Paul Biya, inda ta nuna cewa tsarin siyasar da yake tafiyarwa mai gamsarwa ne.

Ga dukkan alamu tana cikin wadanda za su yi wa jam’iyyar yakin neman zabe. Akan hakane ta sauka birnin Garoua, garin mahaifinta, domin ta rinjayi masu kada kuri’a da su dafa wa jam’iyyar Shugaban kasa baya.  Rahotannin na nuni da cewa ta samu tallafin Sefa Dubu 400,000, kimanin Dala 800, domin ta samu karfin gwiwar kewaye sako-sako wurin rinjayar jama’a. Tuni dai ra’ayin jama’a ya bambanta game da wannan bullowar da Aminatou ta yi wa jam’iyyar RDPC, alhalin lokacin da suka bar kasa tana da shekaru 10 a duniya.
Ra’ayin mutanen kasar ya bambanta, wasu ma har nuna bacin ransu suka yi, domin suna ganin kawai za a yi amfani da ita, wajen jan ra’ayin jama’a.

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan