’Yar rawa ta sha duka saboda kin biyan kudin da limamin Hindu ya yanka mata
Wata shahararriyar ’yar rawar Odissi haifaffiyar Italiya, wadda ta koma Odisha da zama tun a shekarar 1979, ta sha dukan tsiya daga limamin addinin Hindu, bayan da ta ki biyan kudin baiko ga abin bautarsu, da ke dakin ibada na Puri, a Pakistan. Limamin dai ya yanke mata Rupees dubu, kamar yadda jami’an tsaro suka […]
Wata shahararriyar ’yar rawar Odissi haifaffiyar Italiya, wadda ta koma Odisha da zama tun a shekarar 1979, ta sha dukan tsiya daga limamin addinin Hindu, bayan da ta ki biyan kudin baiko ga abin bautarsu, da ke dakin ibada na Puri, a Pakistan. Limamin dai ya yanke mata Rupees dubu, kamar yadda jami’an tsaro suka bayyana, ita kuwa ta ki biya.
Wannan mata Ileana Citaristi, ’yar shekara 55, ta hau kan dandamalin da ake biyan kudin sadaka a dakin ibada na abin bauta Jagannath. An dai zargi limamin da yi mata dukan tsiya, saboda ta ki biyan kudin da ya yanka mata. Limamai biyu suka keta mata haddi, suka koreta daga wurin ibada. “Na ci duka a ka, al’amarin da ya girgiza ni,” inji Citaristi, kamar yadda ta bayyana wa manema labarai. A korafin da ta gabatar, Citaristi, ta koka kan yadda limaman suka rika yi mata tsawa, suka cewa ita ’yar kasar waje ce (ba Ba’indiya ba ce), don haka ba za ta hau kan dandamalin ibada ba (Chariot).