’Yar shekara 64 ta yi ninkayar kilomita 160

Diana Nyad, ’yar shekara 64 ta bude sabon babi a tarihin kurme, inda ta yi ninkayar sa’o’I 53 daga kasar Cuba zuwa Florida ta Amurka, wato nisan kilomita 160. Ta fara wannan ninkaya ne a ranar Asabar ta kare a ranar Litinin da ta gabata. Wannan dai shi ne karo na biyar da Nyad ta […]

’Yar shekara 64 ta yi ninkayar kilomita 160

Diana-Nyad ’yar shekara 64 wadda ta yi ninkayar kilomita 160Diana Nyad, ’yar shekara 64 ta bude sabon babi a tarihin kurme, inda ta yi ninkayar sa’o’I 53 daga kasar Cuba zuwa Florida ta Amurka, wato nisan kilomita 160. Ta fara wannan ninkaya ne a ranar Asabar ta kare a ranar Litinin da ta gabata. Wannan dai shi ne karo na biyar da Nyad ta yi hankoron shafe mil 110 tana ninkaya. Ta fara kwatantawa a shekarar 1978, sai a 2001 da 2012, in da ta cimma burinta a Agustan bana.
Wannan dattijuwa ta shiga tarihi, inda ta tashi da wurin wasan kwale-kwalen alfarma da ke Habana a ranar Asabar, ta isa gabar ruwan Key West da ke Florida. A da kuwa ta sha kwatanta aiwatar da wannan buri nata, har sau hudu, amma guguwa da farmakin manyan kifaye suka hanata kaiwa gaci.
“Na samu sakonnin kwarin gwiwa uku,” a cewar Nyad, lokacin da ta dora kafar a kan doron kasa. “daya na cewa, kada mu nuna gazawa, kada mu kasa. Biyu kuwa, ba ki tsufa da kokarin tabbatar da mafarkinki ba. Na uku kuwa, al’amarin ya kasance tamkar wasan kadaici, amma a kungiyance ake yi,” Nyad ta jinjina wa masu goyon bayanta.
Wannan Ba’Amurkiyya ta samu goyon baya daga mashahuran mutane, wadanda suka hada da Shugaba Barack Obama na Amurka da Hilary Clinton. Sun aike mata da sakonnin taya a murna a shafinta na tweeter. Kada ki rankwafa, har sai mafarkinki ya zama gaskiya,” inji Obama. Ita kuwa Hillary Clinton cewa ta yi, “Ninkayar da kika yi a tsaknin kasashe biyu, tamkar kin karade kasashen duniya 112. Kin sa na dauka cewa ina ninkaya a tsakanin manyan kifayen sharks, amma hakika haka kika aikata. Muna murana!”

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan