Ƙananan Hukumomi: Kotu ta dakatar da sayar wa ’yan takara fom a Kano

An ƙayyade naira miliyan 10 ga masu neman shiga zaɓen ciyaman da kuma naira miliyan biyar ga masu takarar kujerar kansila.

Ƙananan Hukumomi: Kotu ta dakatar da sayar wa ’yan takara fom a Kano

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta dakatar da sayar wa ’yan takara fom ɗin shiga zaɓen ƙananan hukumomin Kano.

Kotun ta miƙa wannan umarni ne ga Hukumar Zaɓen Kano (KANSIEC) wadda ta ƙayyade farashin naira miliyan 10 ga masu neman shiga zaɓen kujerar shugaban karamar hukuma da kuma naira miliyan biyar ga masu neman shiga takarar kujerar kansila.

A wannan Larabar ce Alƙalin Kotun, Mai Shari’a Emeka Nwite ya bayar da umarnin yana mai sanya 15 ga watan Satumba a matsayin ranar da za a soma sauraron ƙara.

Aminiya ta ruwaito cewa, wasu jami’yyun siyasa da suka haɗa da APP da ADP da SDP ne suka yi ƙarar Hukumar ta KAINSEC a gaban kotun kan abin da suka kira tsawwala farashin fom ɗin takara domin hana su shiga zaɓen.

Idan za a iya tuna cewa, a watan Agustan da ya gabata ne KANSIEC ta sanya cewa dukkanin mai son ya yi takarar kujerar ciyaman zai biya Naira miliyan 10 yayin da mai sha’awar takarar kujerar kansila zai sayi fom kan Naira miliyan biyar.

Hukumar KANSIEC dai ta tsayar da 26 ga watan Oktoba a matsayin ranar da za ta gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin a Jihar Kano a maimakon 30 ga Nuwamba da ta sanya da farko.