Ƙaranci mai ya yi ƙamari a Kano, Kaduna da Katsina

NNPCL ya ce ƙarancin man na da alaƙa da rashin kyawun yanayi da aka fuskanta a baya-bayan nan.

Ƙaranci mai ya yi ƙamari a Kano, Kaduna da Katsina

A Jihohin Kano, Kaduna da Katsina, ƙarancin man fetur na ƙara yin ƙamari, lamarin da ya sanya masu ababen hawa shiga tsaka mai wuya.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN), ya ruwaito cewa yawancin gidajen mai sun rufe, kuma kaɗan daga cikin waɗanda suke aiki suna sayar da mai a kan Naira 800 zuwa Naira 1000 kan kowace lita.

Wannan ya haifar da mawuyacin hali ga mazauna jihohin, inda farashin mai a wajen ’yan bunburutu ya kai Naira 5000 zuwa Naira 6000 kan galan mai cin lita huɗu.

Direbobi da yawa sun nuna rashin jin daɗinsu, inda suka bayyana cewar ƙarancin ya haifar musu da koma baya.

Wani ma’aikacin gwamnati, Salisu Baso, ya ce kuɗin sufuri ya ninka sau biyu, wanda hakan yake masa wuya zuwa wajen aiki wasu lokutan.

Ya soki gwamnati da ‘yan kasuwa kan wannan matsalar, inda ya yi kira da a ɗauki matakin gaggawa don warware matsalar.

Wata ’yar kasuwa Misis Francisca Idika daga kasuwar Chechnya a Jihar Kaduna, ta bayyana yadda ƙarancin ya shafi kasuwancinta.

Ta ce tsadar kuɗin sufuri, ya shafe ta da sauran ‘yan kasuwa, wand hakan ya tilas su ƙara farashin kayayyakinsu.

A cewarta hakan ya sa farashin kayayyaki ya ƙaru ga kwastomomi.

A Kano da Katsina haka lamarin yake, inda ko ina ka bi za ka iske dogayen layuka da kuma tsadar mai.

Wani ƙwararre a hakar kimiyya da fasaha, Alao Jaremi da wasu mazauna jihohin, sun yi kira ga hukumomi da su magance matsalar cikin gaggawa don rage wahalhalun da ‘yan Najeriya ke ciki.

Kamfanin Mai na Ƙasa na Najeriya (NNPCL) da ’yan kasuwar na zargin juna kan ƙarancin mai, amma a gefe ɗaya kamfanin man ya ce matsalar yanayi ce ta haifar da ƙarancin man.

Kashim Shettima zai jagoranci tawagar Nijeriya a taron MDD

NECO ta fitar da sakamakon jarrabawar 2024

Kano: Abba ya rusa ciyamomin riko

An haramta wa ma’aikatan Asibitin Tarayya yin ‘kirifto’ a wurin aiki