Ƙarancin Ruwa: An raba wa masu rijiyoyin burtsatse kyautar man dizel a Yobe

Kwanan nan gwamnati ta ƙara samar da man dizel daga lita 40,000 zuwa lita 60,000.

Ƙarancin Ruwa: An raba wa masu rijiyoyin burtsatse kyautar man dizel a Yobe

Gwamna Mai Mala Buni

Gwamna Mai Mala Buni na Jihar Yobe, ya umurci ma’aikatar ruwa da ta samar da man Dizel kyauta ga masu rijiyoyin burtsatse masu zaman kansu duk mako a birnin Damaturu da kewaye.

Wannan wani yunƙuri ne na bunƙasa samar da ruwan sha ga mazauna birnin Damaturu da kewaye.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da hadimin sadarwa na Gwamnan Yobe, Yusuf Ali ya fitar yayin da yake sa ido kan rabon man dizel ɗin a ranar Litinin.

Babban Manajan Kamfanin Ruwa na Jihar, Injiniya Mahdi Zarma ya bayyana cewa ana ƙoƙarin rage farashin kurar ruwan da ke yi wa jama’a dakon ruwan jihar.

“Kwanan nan gwamnati ta ƙara samar da man dizel daga lita 40,000 zuwa lita 60,000 zuwa sama da rijiyoyin burtsatse 100 a Damaturu, da kewaye.

“Amma mun fahimci cewa wasu yankunan da ke da yawan jama’a  har yanzu suna fuskantar ƙalubalen samun ruwa a farashi mai rahusa daga masu Moya da ke ɗaukar ruwa zuwa gidajen Mutane.

“Muna bai wa wasu zaɓaɓɓun kowace rijiyar burtsatse ta masu zaman kansu da ke Damaturu kowace lita 10 na dizal domin rage raɗaɗin masu saye.

“A cikinsu akwai masu karɓar Naira 300 kan kowace kurar ruwa wadda hakan ya tilasta wa masu tallan ruwan sayar da kurar ruwa a kan kuɗi kusan Naira 1,000 ga mazauna wurin, don haka da wannan ci gaban, muna fatan za su rage kuɗin ga  jama’a ko masu saye”.

Adamu Abubakar, wani ma’aikacin rijiyar burtsatse mai zaman kansa da kuma Babagana Ali mazaunin unguwar Nasarawa da ke Damaturu, sun miƙa godiya ga gwamnati kan yadda ta rage raɗaɗin da jama’a ke fama musamman a wannan lokaci na zafi.

Babban Manajan hukumar Ruwan ya ce sama da rijiyoyin burtsatse 100 masu zaman kansu za su ci moriyar man dizal kyauta domin haɓaka samar da ruwa a Damaturu da kewaye gaba ɗaya.