Ƙarin Kuɗin Fetur: Tsadar Kayayyaki Na Iya Ƙaruwa —MAN

Ƙarin farashin ya haifar da martani a duk faɗin ƙasar inda ƙungiyoyin ma’aikata ke neman a soke sabon farashin nan take.

Ƙarin Kuɗin Fetur: Tsadar Kayayyaki Na Iya Ƙaruwa —MAN

An ƙara farashin man fetur a Najeriya

Kungiyar Masana’antu ta Najeriya (MAN) ta ce akwai yiwuwar a samu ƙarin hauhawar farashin kayayyaki, a sakamakon karin kuɗin mai a ƙasar.

Kungiyar ta kuma ce Ƙananan Kamfanoni da Matsakaitan Kamfanoni (SMEs), waɗanda galibi ke gudanar da harkokinsu da matsakaitan jari na iya ci gaba da fuskantar ƙalubale.

An samu ƙarin farashin man fetur a ranar Talata daga kusan Naira ₦568 kan kowace lita zuwa ₦855,  a gidajen mai na kamfanin NNPC.

Ƙarin farashin ya haifar da martani a faɗin ƙasar inda ƙungiyar ma’aikata ke neman a soke sabon farashin nan take.

A ranar Laraba, Ƙungiyar MAN, a cikin wata sanarwa da Babban Daraktanta, Segun Ajayi-Kadir, ya fitar, ya bayyana ilkar ƙarin farashin man fetur.

“Tasirin da zai iya kasancewa ya haɗa da ƙaruwar farashin sufuri da na kayayyaki da na ayyuka.

“Sakamakon farashin man fetur da ya ƙaru, masu amfani da su za su kashe kuɗi da yawa kan harkokin sufuri da makamashi, tare da barin su da ƙarancin kuɗin shiga.

“Wannan na iya kawo raguwar kuɗaɗen siyayyar kayayyaki da ayyuka, wanda ke shafar kasuwanci a sassa daban-daban.

“Waɗannan alamu ne na yiwuwar hauhawar farashin kayayyaki, da yin tasiri kan ƙarfin aljihun magidanta,” in ji shugaban.

Ya nuna damuwarsa cewa, “Ko shakka babu zai ƙara haddasa tsadar kayayyaki.

“Waɗannan za su haifar da hauhawar farashi da kuma fuskantar raguwar kuɗin shigar da talakawan Najeriya ke fuskanta,” in ji Ajayi-Kadir.

Kirsimeti: FRSC ta aike jami’ai 1,539 zuwa Kano

Gwamnatin Kano na shirin tara harajin 80bn a 2025

Kirsimeti: Zulum ya ɗauki nauyin jigilar fasinjoji 710 zuwa garuruwansu

Ɗan shekara 60 ya rasu a hatsarin kwalekwale a Sakkwato