Ƙayyade Shekarun Shiga Jami’a Daidai Ne —Majalisa
Majalisar Dattawa ta goyi bayan aiwatar da dokar sanya shekaru 18 a matsayin mafi karanci ga dalibai masu shiga jami’a
Majalisar Dattawa na shirin farfado da dokar sanya shekaru 18 a matsayi mafi karanci ga dalibai masu shiga jami’a da sauran manyan makarantun Najeriya.
Shugaban kwamitin majalisar mai kula da manyan makarantu da TETFund, Sanata Muntari Dandutse Kwamitin, ya ce nan ba da dadewa ba majalisar za ta yi dokar kayyade shekarun shiga manyan makarantu.
Sanata Muntari Dandutse ya sanar da haka ne bayan zagayen da shi da ’yan kwamitin na majalisar dattawa da ta wakiliai suka yi a cibiyon zana jarrabawar shiga manyan makarantu da hukumar JAMB ta gudanar a Abuja.
Dan majalisar ya yaba da matakin da Ministan Ilimi, Farfesa Tahir Mamman, ya dauka na kayyade shekaru 18 a matsayin mafi karanci ga masu shiga makarantun gaba da sakandare, da cewa hakan zai hana kananan yara shiga jami’a.
- Mun kama mahaifin da ya zana wa ɗansa jarrabawa — JAMB
- Emefiele Ya Kashe N18.9bn Kan Buga Sabbin N684.5m —EFCC
Ya jinjina wa hukumar JAMB kan yadda ta shirya jarabawar da ake gudanarwa a matsayin abin burgewa.
Sanata Sunday Karimi, mamba a kwamitin majalisar dattawa kan manyan makarantu da TETFund, ya ce kayyade mafi karancin shekarun ba zai yi illa ga bukatar inganta harkar ilimi a Najeriya ba.
“Ya kamata kowa ya samu damar samun ilimi. Don mutum ya kai shekara 40 ko 50 ba ya nufin ba zai iya shiga jami’a ba; amma kuma yana da kyau a sanya mafi karancin shekarun shiga.
“Ba zai yiwu dan shekara 12 ko 13 kai ko 14 ma ya ce wai so yake ya shiga jami’a ba.
“Muna goyon bayan ministan ilimi kan sanya shekara 18 ga masu neman shiga jami’a, domin kafin ka shiga firamare sai ka kai 6, kafin ka shiga sakandiare sai ka kai 12, don haka kafin ka shiga jami’a dole ne ka zama akalla kana da shekara 18.”
Da yake magana kan dokar cika shekara 18 kafin shiga manyan makarantu, Sanatan ya ce, “Dokar na nan, kuma tana aiki, idan akwai bukatar a yi mata wata gyara don tabbatar da tana da karfi, to tabbas za mu yi hakan.”
Shugaban kwamitin majalisar wakilai, Oforji Oboku, da yake jawabi ga wasu ɗalibai a makarantar gwamnati ta Tudun Wada, Abuja, ya yi kira gare su da su yi abin da ya dace domin yin nasara a jarrabawar.
Kazalika ya bayyana farin cikinsa kan kwazon daliban da cewa hakan ya nuna Najeriya na da makoma mai haske, ya kuma shawarce su da su ci gajiyar tsarin ba da lamuni ga dalibai idan suka shiga manyan makarantu.