Ƙudirin gyara Dokar Masarautun Kano ya tsallake karatun farko
Jam’iyyar NNPP ta kammala shirinta na rusa Masarautar Bichi tare da dawo da Sarki Sanusi kan karagarsa.
Ƙudirin gyara dokar Masarautun Kano ya tsallake karatun farko yayin da Majalisar Dokokin jihar ta soma zama kan batun a wannan Larabar.
Aminiya ta ruwaito cewa, jami’an tsaro ɗauke da makamai da suka haɗa da ‘yan sanda da na sibil difens ne suka mamaye wasu muhimman wurare a harabar Majalisar Dokokin a ranar Laraba, yayin da ‘yan majalisar suka fara gyaran dokar majalisar masarautun jihar da ta kafa masarautu biyar.
An soma zaman yi wa dokar kafa masarautun gyara yayin da shugaban masu rinjaye kuma mamba mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Dala, Lawan Hussaini Chediyar ’Yan Gurasa ya gabatar da ƙudirin.
Aminiya ta ruwaito cewa, hatta manema labarai da suka zo cin kasuwar ɗaukar rahoton zaman majalisar na wannan rana sai da aka riƙa tantance su gabanin samun izinin shiga harabar majalisar sa jami’an tsaro suka yi wa dandazo.
Sai dai shugaban marasa rinjaye na majalisar, Abdul Labaran Madari, ya shaida wa BBC cewa ’yan jam’iyyar APC 12 a majalisar ba sa adawa da gyaran matuƙar ba za a rusa ko ɗaya daga cikin masarautun biyar ba.
Haka kuma, Madari ya ce ba za su yi adawa da yi wa dokar gyaran fuska ba matuƙar ba za a tsige Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero ba kuma ba za a maye gurbinsa da Sarki Muhammad Sanusi ba.
Ya ce duk da cewa ’yan majalisar na jam’iyyar NNPP suna da adadin da za su aiwatar da gyaran, sai dai hakan ba zai hana su adawa ba.
Madari ya ce yana zargin jam’iyya mai mulki ta kammala shirinta na rusa Masarautar Bichi tare da maido da tsohon Sarki Sanusi yayin da za a bai wa sauran masarautun hakimancin ƙananan hukumomi uku-uku kacal.
A watan Disambar 2019 ce gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta yi wa dokar masarautun jihar gyara, inda aka ƙirƙiro ƙarin masarautu gudu huɗu masu daraja ta ɗaya.
Masarautun sun haɗa da Gaya da Ƙaraye da Rano waɗanda aka ɗaga darajarsu zuwa masu daraja da ta ɗaya daidai da masarautar Kano.
Sai kuma Masarautar Bichi da aka ƙirƙiro, abin da ya sa Kano ta zama tana da masarautu biyar masu daraja ta ɗaya.
Masu adawa da matakin a lokacin sun soki ƙirƙiro sababbin masarautu a Kano domin a cewarsu hakan zai rusa tarihin masaratuar Kano na daruruwan shekaru, inda masarautar take da ƙima a idon duniya saboda faɗinta da kuma tasirinta.
Amma mutanen yankunan da aka ƙirƙiro wa masarautun sun yi maraba da matakin, suna cewa hakan zai ƙara kawo musu ci gaba da bunƙasa.
An dai jima wasu ɓangarori na kiraye-kirayen dawo da Sarkin Kano na 14, Muhammadu Sanusi II kan kujerarsa wanda gwamnatin da ta gaba ta tuɓewa rawani.