Ƙudirori 10 da suka yi amo a dimokuraɗiyyar Nijeriya

A cikin shekaru 25 Majalisar Dokokin Tarayya ta amince da ƙudirori 816.

Ƙudirori 10 da suka yi amo a dimokuraɗiyyar Nijeriya

Tun dawowar mulkin dimokuradiyya a Nijeriya a 1999, Majalisar Dokoki ta Kasata shekara 25 tana gudana ba tare an katse ta ba, inda ta amince da kudirori sama da 800 da suka zama dokoki.

Aminiya ta dauki goma daga cikin wadannan kudirori na majalisar da ta hada da ta wakilai da kuma ta dattijai.

A wajen akasarin ’yan majalisa, aikin ’yan majalisa na ɗaya daga cikin wanda aka fi caccaka da yi masa mummunar fahimta a tsakanin ɓangarorin gwamnati.

Su ne suke shan suka daga jama’ar kasa musamman a kan batun albashi ko alawus dinsu wanda wasu ke ganin sun yi yawa. Kuma a lokuta da dama ana zarginsu da zama ’yan amshin shata.

Duk da cewa ra’ayi ya bambanta a kan ko majalisa ta fi shan suka a lokacin dimokuradiyya ko a’a, dole a yarda cewa ɓangaren majalisa ne ya fi wulakanta a duk lokacin da sojoji suka yi kutse a harkokin siyasar kasar nan.

Saboda a duk lokacin da sojoji suka yi juyin mulki, majalisa suke fara rushewa a matakin jiha da tarayya.

Amma daga 1999 Majalisar Dokoki ta Kasa ta yi rubu’in karni wato shekara 25 ba tare da yi mata kutse ba.

A cikin waɗannan shekaru majalisar ta amince da ƙudirori 816 da shugabannin kasa daban-daban suka sa wa hannu.

A Majalisa ta 4 daga 1999 zuwa 2003, Majalisar Dattawa ta amince da kudirori 65, yayin da Majalisar Wakilai ta amince da 112, sannan ’yan majalisar sun yi ittifaki a kan kudirori 65 kadai.

An samu ci gaba a Majalisa ta 5, wadda ta amince da kudirori 129.

Adadin ya ragu a Majalisa ta 6 zuwa kudirori 72, kafin ya sake cirawa sama a Majalisa ta 7 da kudirori 128, sai a Majalisa ta 8 aka samu waɗanda suka fi na kowane lokaci har guda 282, kafin su sauko zuwa 134 a Majalisa ta 9.

A kasa ga wasu daga cikin manyan kudirorin da aka amince da su a wannan tsakani:

Dokar Harkar Man fetur

Bayan shekaru ana ta ce-ce-ku-ce da jan kafa a kan kudirin Dokar Man Fetur, a shekarar 2021 an amince da dokar wadda tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sa wa hannu.

An fara gabatar da kudirin ne ga majalisa a shekarar 2008.

A cewar wata takarda da wani kamfani mai suna Price watch house Coopers International Limited ya gabatar ya ce dokar ta samar da yadda za a gudanar kuma a sa-ido da tafiyar da harkokin kudi na ɓangaren harkokin man fetur a Nijeriya bisa doka da kuma yadda za a bunkasa yankunan da suke samar da man.

Majalisar Dattawa ta 9 ta amince da kudirin a ranar 15 ga Yulin 2021, Majalisar Wakilai kuma ta amince a ranar 16 ga Yulin, wanda hakan ya kawo karshen ce-ce-ku-cen da ake ta yi a kan kudirin da nufin kawo ci gaba ga kasa.

Dokar Bayar da Bayanai (FOI Act)

Wannan kudiri na bayar da bayanai (FOI) wata nasara ce da majalisar ta samu da ya tabbatar da tafiyar da gwamnati.

Wannan doka za ta taimaka ne wajen bai wa ’yan kasa damar samun bayanai daga gwamnati kan yadda ake tafiyar da ayyuka.

Da farko an gabatar da kudirin ne a 1999. Wannan kudiri ya bi matakai da dama inda aka rika yin gyara a kansa har sai da Shugaba Jonathan ya rattaba hannu ya zama doka a ranar 28 ga watan Mayun 2011.

Wannan doka ta bai wa ’yan kasa damar samun bayanai daga gwamnati ko hukumomin gwamnati.

’Yan jarida da lauyoyi da kungiyoyi masu zaman kansu sun yi amfani da dokar wajen tabbatar da hukumomin gwamnati da shugabanin suna yi abin da ya dace.

Sai dai akwai damuwa kan rashin kin bin dokar daga wasu hukumomin gwamnati.

A shekarar 2021, Majalisar Wakilai ta ce akalla hukumomin gwamnati 73 ne daga cikin 93 suke bin umurnin dokar wajen ba da bayanai.

Ƙudirin ƙin amincewa da auren jinsi

Wannan wani kudiri ne da majalisa ta amince da shi kuma Shugaban Kasa Jonathan ya rattaba wa hannu a wani yunƙuri na kin amincewa da matsi daga gwamnatocin kasashen Turai cewa dole Nijeriya ta mutunta ’yancin ’yan luwadi da madigo.

A ranar 29 ga watan Nuwamban 2011 Majalisar Dattawa ta amince da kudirin dokar haramta auren jinsi a Nijeriya, sai Majalisar Wakilai ta amince a ranar 30 watan Mayun shekarar 2013.

Sannan a watan Janairun shekarar 2014, Jonathan ya sa hannu a kan kudirin ya zama doka.

Kafin wannan lokaci an gabatar da kudirori biyu da su ma ba a amince da su ba a kan amincewa da auren jinsin.

Dokar ta haramta auren jinsi ta kuma haramta kungiyoyi da ke goyon bayan auren jinsi, sannan ta tanadi hukuncin daurin shekara 14 ga duk wanda aka samu da aikata daya daga cikin laifuffukan.

Amincewa da rattaba hannu kan amincewa da kudirin ya samu goyon bayan al’ummar kasa kuma yana daya daga cikin nasarorin gwamnatin Jonathan.

Sai dai gwamnatin ta sha suka domin wasu masana siyasa na ganin kin amincewa da dokar ya sa kasashen Turai kin sayar wa Nijeriya makamai da kin goyon bayan gwamnatinsa duk da hare-haren da Boko Haram ke kaiwa a kasar nan.

Wasu ma na ganin hakan ya taka rawa wajen faduwar gwamnatin Jonathan a zaɓen shekarar 2015.

Ƙudirin Ba Matasa Damar Tsayawa Takara

Majalisar Dokoki ta Kasa ta amince da kudirin kamar yadda sassa na 65, 105, 132 da 177 na Kundin Tsarin Mulkin 1999 da aka gyara ya tanada.

Dokar ta janye wasu tsauraran sassa a cikin Kundin Tsarin Mulki. Ta rage shekarun tsayawa takarar Shugaban Kasa daga 40 zuwa 30, gwamnoni daga 35 zuwa 30 sanatoci daga 35 zuwa 30,

Majalisar Wakilai daga 35 zuwa 25 sai majalisun jihohi daga 30 zuwa 25.

A watan Yulin shekarar 2017 majalisar ta amince da kudirin aka mika ga Shugaban Kasa don sa hannu kuma a watan Afrilu shekarar 2018.

Kuma a ranar 31 ga watan Mayun shekarar 2018, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sa hannu a kai. Tun daga lokacin aka samu matasa da dama da aka a zaɓa a majalisun dokoki.

Daga cikin wadanda suka amfana da dokar akwai, Ibrahim Mohammed mai shekara 28 mai wakiltar Mazaɓar Birnin Kebbi, Kalgo da Bunza a Majalisar Wakilai, inda ya zama daya daga cikin wadanda ake kwatance da su.

Ƙudirin Kula da Naƙasassu

Manufar kudirin ita ce a kawar da nuna bambanci ga nakasassu, inda aka amince da shi a shekarar 2016.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ne ya sa hannu ya zama doka a ranar 23 ga watan Janairun 2019.

Wannan doka ta haramta duk wani nau’i na nuna bambanci ga nakasassu, inda aka tanadi tarar Naira miliyan daya ga kamfani ko Naira dubu 100 ga daidaikun mutane ko zaman gidan yari na wata shida ga duk wanda ya karya dokar.

Ƙudirin kafa Hukumar Bunƙasa Arewa maso Gabas

Tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ne ya rattaba hannu don kafa Hukumar Bunkasa Arewa maso Gabas (NEDC) a watan Oktoban shekarar 2017, shekara guda bayan majalisa ta amince da kudirin.

Wannan kudiri ana yi masa kallon kudiri mai mahinmanci musamman idan aka yi la’akari da irin ɓarnar da rikicin Boko Haram ya janyo wa yankin.

Bayan kafa hukumar alhakinta ce ta yi amfani da kudaden da Gwamnatin Tarayya za ta ba ta ko na kungiyoyin kasashen waje don sake tsugunar da ’yan gudun hijira da sake gina yankin da samar da hanyoyin mota da gidaje da wuraren kasuwanci ga wadanda rikicin ya shafa.

Sannan dokar ta ba da damar a nemo taimako domin magance matsalar talauci da ta yanayi a Arewa maso Gabas.

Majalisar Dattijai ta amince da kudirin a watan Oktoban 2016 tare da keɓe mata kashi uku cikin 100 na harajin kayan bukatu (VAT) na Gwamnatin Tarayya.

Ƙudirin Masu Fallasa Ɓarayin Gwamnati da Ba su Kariya

A watan Yulin shekarar 2017, Majalisar Dattijai a karkashin Shugabanta Bukola Saraki ta amince da kudirin bai wa irin wadannan mutane kariya.

Kudirin wanda ya ba da kwarin gwiwa domin bayyana irin taɓargaza da wasu jami’an gwamnati ke aikatawa, ya ba da kariya ne ga duk wanda ya ba da irin wadannan bayanai a hukumance.

Kudirin ya zo ne a watan Afrilun shekarar 2017 a lokacin da Hukumar Yaki da Yi Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) ta gano Dala miliyan 43.3 da wasu kudaden kasashen waje a cikin wani gini a Ikoyi da ke Jihar Legas.

Hukumar EFCC ta danganta wannan nasara da yaba wa wanda ya fallasa wajen ajiyar. Shugaban Kasa Muhammadu Buhari bai rattaba hannu a kan kudirin ba.

Amma Gwamnatin Tarayya ta samar da tsarin saka wa masu ba da bayanan a wani yunkuri na yaki da cin hanci da rashawa.

Ƙudirin Kiwon Lafiya na Ƙasa

An amince da kudirin ne a Majalisa ta 7, inda kuma Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ya rattaba wa hannu a watan Disamban shekarar 2014.

Dokar ta yi cikakken bayanin irin rawar da kowane sashe na gwamnati zai taka a kan abin da ya shafi kiwon Lafiya.

Manufa ita ce a taimaka wa Nijeriya ta cim ma nasarar inganta kiwon lafiya, ta kuma rika sa idanu a kan sashen tare da tabbatar da kwarewa a tsakanin ma’aikatan kiwon lafiya.

Ta kuma sanya ka’idoji a kasa baki daya da nufin rage ko kawar da ma’aikatan bogi a sashen kiwon lafiya.

Wannan doka ta kuma samar da tsarin inshorar lafiya ga ’yan Nijeriya musamman marasa galihu an sake gyara a dokar a shekarar 2022.

Ƙudirin Bai wa Ɗalibai Rance

Wannan kudiri Majalisa ta 9 ce ta amince da shi wanda tsohon Shugaban Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila ya gabatar.

Sannan Shugaban Kasa Bola Tinubu bayan ya hau mulki a ranar 12 ga watan Yunin 2023, ya rattaba hannu a kai ta zama doka domin bai wa daliban Nijeriya damar karɓar rance su yi karatu ba tare da ruwa ba.

Har ila, yau Shugaban Kasa a watan Maris na bana ya rubuta wa majalisa yana neman yin gyara ga dokar domin cire duk wasu ka’idoji da ka iya zama cikas wajen aiwatar da ita.

Don haka a ranar 20 ga watan Maris Majalisar Dattijai da ta Wakilai suka amince da kudirin ba da rance ga dalibai a manyan makarantu wanda aka yi gyara a 2024.

Kudirin ya tsallake karatu na farko da na biyu da na uku a zaman da aka yi a ranar 3 ga Afrilu, inda Shugaban Kasa Tinubu ya rattaba hannu a kan dokar da aka yi wa gyara ta 2024.

Ƙudirin Mafi Ƙarancin Albashi na Ƙasa

Bayan tattaunawa da zanga-zanga da tarurruka a tsakanin kungiyoyin kwadago da gwamnati na kusan shekara biyu, Majalisar Dattijai ta amince da mafi karancin albashi na Naira dubu 30 a shekarar 2019 kuma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sa hannu ta zama doka tare da umartar aiwatar da dokar a ranar 18 ga Afrilun 2019. Shekara biyar bayan an ci gaba da tattauna batun sabon mafi karancin albashi na kasa.

Ƙudirin lalura

Kudirin lalura na ginuwa ne don daukar wani mataki da ba saban ba da wata hukuma mai iko ke amfani da shi don dawo da doka da oda da kare muhimman ginshikan Tsarin Mulki, kuma ana daukar hakan a matsayin halattacce koda ya karya wasu ka’idoji da dokoki da alkawura.

Wannan doka ba kudiri ba ne da majalisa ta amince da shi, a’a wasu ginshikai ne da aka yi aiki da su alokacin rashin lafiyar marigayi Shugaban Kasa Umaru Musa ’Yar’aduwa a shekarar 2010, wanda ya zama zance mai muhimmanci a Majalisar Dokoki ta Kasa tun 1999.

A lokacin marigayi Shugaban Kasar ya gaza aiwatar da aikinsa saboda rashin lafiya kuma yana kasar waje don jinya a shekarar 2009 da 2010, kuma bai mika ragamar mulki ga Mataimakinsa Goodluck Jonathan kamar yadda doka ta tanada ba, yana waje na tsawon watanni, hakan ya dora kasar a daf da fadawa cikin rudanin Tsarin Mulki.

Majalisar Dattijai ce ta dauki wannan mataki ta amince Jonathan ya zama Shugaban Kasa na riko.

Wannan mataki ya yi matukar daidaita al’amura a kasar nan, ya sa majalisar ta yi martaba a idon ’yan Nijeriya musamman a Kudancin kasar nan.

’Yar’aduwa ya rasu a ranar 5 ga watan Mayun shekarar 2010, shi kuma Jonathan ya haye kujerar a matsayin Shugaban Kasa mai cikakken iko.