Ƙuncin Rayuwa: Hatta wasu ministocin ba su da ikon ganin Tinubu — Ndume
Mu na tsoron kar wata rana a tashi ko mutum na da kuɗin sayen abincin, ya je kasuwa amma ba zai samu ba.
Bulaliyar Majalisar Dattawa, Sanata Ali Ndume, ya ce duk da halin matsi da ƙuncin rayuwa da ake fuskanta a ƙasar a yanzu, akwai ministocin da ba su da ikon ganin Shugaba Bola Tinubu domin tattauna matsalar har a samu damar yi wa tufkar hanci.
Da yake zantawa da BBC Hausa, Sanata Ndume ya bayyana cewa babbar matsalar da ake fama da ita a wannan gwamnati ita ce ƙofar su a rufe take yadda hatta wasu ministocin ba sa iya ganin shugaban ƙasa, bare ’yan majalisa ma su samu zarafin ganawa da shi da bayyana abubuwan da ke faruwa a yankunan da suke.
- Gomman ’yan Boko Haram sun miƙa wuya a yankin Tafkin Chadi
- Kawu Sumaila ya miƙa ƙudirin ƙirƙiro sabuwar jiha daga Kano
Sanatan na magana ne jim kaɗan bayan sun gabatar da wani ƙudurin haɗin gwiwa tsakaninsa da takwaransa Sanata Sunday Steve Karimi, suna cewa hukumar abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi gargaɗin mutum miliyan 82 za su yi fama da matsalar abinci a Nijeriya nan da shekara biyar masu zuwa.
Sanata Ndume ya ce manufar ƙudirin ita ce, janyo hankalin mahukuntan ƙasar su san matsalar yunwar da ake fuskanta a Najeriya baki ɗaya, kamar yadda shirin samar da abinci na Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi gargaɗi, wanda a bana ne aka sanya Nijeriya cikin ƙasashen da za su fuskanci yunwa a duniya.
“Mun yi da nufin tayar da gwamnati ko tunatarwa idan ba su sa ni ba, su san cewa a cikin Nijeriya fa ba wai hauhawar farashin kaɗai ake fama da shi ba, har da rashin abincin.
“Mu na tsoron kar wata rana a tashi ko mutum na da kuɗin sayan abincin, ya je kasuwa amma ba zai samu ba.
“Mun samu labari a Jihar Katsina, idan an fara yunwa a ƙasa kananan yara ne ke fara jin jiki, yara sun fara fama da ƙarancin abinci mai gina jiki, yanayi ne da ke faruwa a wuraren da ake fama da yaƙi ko fari.
“Mun ga yadda ya faru a Jamhuriyar Nijar, da Sudan ta Kudu, inda yara ke mutuwa sanadiyyar yunwa, ka ga mun fara ganin hakan a Nijeriya,” in ji Ndume.
Ya ce abin da suke son gwamnati ta yi shi ne ta zauna da masana da sauran ’yan kasa domin sanin yadda za a tunkari matsalar, domin babbar barazanar ita ce a baya gwamnati na tara abinci a cikin rumbunta domin buƙatar lokaci irin wannan.
To amma a yanzu babu wannan, ya ce abin ya zama babban tashin hankalin da ake buƙatar ɗaukar matakin gaggawa kan hakan.
Wasu rahotanni na cewa gwamnatin Nijeriya ta sanar da za a ɗauki kwanaki 150 ana shigar da kayan abinci ƙasar ba tare da biyan kuɗin haraji ba.
Sai dai Sanata Ndume ya ce; “Na ga wannan rahoto amma da na bincika, sai na samu cewa gwamnati ta ce ba haka labarin yake ba, ko ta janye, ko ma menene ya kamata a fito ƙarara a gani a ƙasa.
“Abu na biyu kuma duk fa abin da gwamnatin nan ke yi ya kamata a gane gwamnatin jama’a ce domin jama’a, wannan ita ce dimukuradiyya.
“Ya kamata duk abin da za a yi ya kasance an yi tare da jama’a, su san abin da ake ciki, a tabbatar an kwantarwa da mutane hankali.”
Majalisar Dattijan Najeriyar dai ta nemi gwamnatin ƙasar ta ɗauki matakin gaggawa kan matsalar tashin farashin abinci da kuma rashin wadatarsa da ke daɗa jefa talakawan ƙasar cikin mawuyacin hali.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ’yan ƙasar ke fama da tsadar rayuwa da farashin kayan masarufi musamman kayan abinci, da man fetur wanda yana ɗaya daga cikin abin da ake ganin ya ƙara tsadar komai a ƙasar.