Ƙungiya ta raba wa marayu da mabuƙata kayan makaranta a Kano

Ƙungiyar ta ce ta raba tallafin ne domin kyautata goben yaran.

Ƙungiya ta raba wa marayu da mabuƙata kayan makaranta a Kano

Ƙungiyar Youths for Progressive Union (YUO), ta raba wa yara marayu da masu ƙaramin ƙarfi a unguwar Kofar Mata da ke Jihar Kano, kayayyakin makaranta.

Kayayyakin sun haɗa da littattafai, alƙalami, jakunkuna, da sauran kayan koyo don taimaka wa yaran da iyayensu suka rasu ko kuma ba su da ƙarfi.

Sakataren ƙungiyar, Kwamared Usman Bello Kofar Mata, ya ce sun bayar da taimakon ne, domin rage yawan yara da ke gararamba a tituna, musamman marayu.

“Mun ga yadda wasu yara ke shiga tsaka mai wuya bayan rasuwar iyayensu.

“Wasu ba su da kowa da zai kula da su, sai dai su riƙa yawo kamar awaki. Don haka, muka yi bincike muka zaƙulo irin waɗannan yara don mu taimaka musu,” in ji shi.

Taron rabon kayayyakin ya samu halartar mai unguwar Kofar Mata, Alhaji Muhammad Jibril, wanda ya yi kira da a riƙa taimakon marayu da mabuƙata domin hana lalacewar tarbiyyar yara a yankin.

Ya ce rashin irin wannan taimako ne ke janyo koma-baya a yankin Arewa, inda ya bayar da misali da Kudancin Najeriya inda ake ɗaukar nauyin marayu har su girma su zama mutane nagari a rayuwa.

“Idan har ba a taimaka wa marayu da mabuƙata ba, za su tashi babu tarbiyya.

“Idan yaro ba shi da gata, babu wanda zai gyara masa hanya. Amma idan ana tallafa masa, zai girma da sanin darajar rayuwa,” in ji shi.

Ya buƙaci iyaye da al’umma su ci gaba da kula da tarbiyyar yara tare da basu kulawa da taimako domin su zama mutane nagari da za su amfanar da al’umma.

Dangote ya rage farashin man fetur zuwa N825 a Legas

Na gaji bashin 8.9bn a matsayin shugaban APC — Ganduje

Boko Haram sun sace mutum 2 da kayan abinci a Borno

Buhari da El-Rufai ba su halarci babban taron APC ba