Ƙungiya ta rage farashin kayan marmari saboda Azumin Ramadan

Za mu yi ragin ne daidai gwargwado daga cikin ribar da muke samu saboda albarkar wannan wata.

Ƙungiya ta rage farashin kayan marmari saboda Azumin Ramadan

Shugaban Kungiyar ’Yan Kasuwa Masu Hada-hadar Kayan Marmari a Jihar Oyo, Walin Ibadan, Alhaji Dauda Shehu ya ce, kungiyar za ta rage farashin kayan marmari domin samun sauƙi ga al’ummar Musulmi a cikin watan Azumin Ramadan.

Ya ce, “kamar yadda muka saba yi a baya a irin wannan lokaci, a bana ma za mu rage farashin kayan marmari kamar dankalin Turawa da karas da kukumba da latas da koren tattasai da ake fataucin su daga wasu jihohin Arewa zuwa Kudancin kasa.

“Za mu yi ragin ne daidai gwargwado daga cikin ribar da muke samu saboda albarkar wannan wata’’, inji shi.

Da yake zagayawa da Aminiya sassa daban-daban na kasuwar kayan marmari ta Benjamin da ke Eleyele a Ibadan babban birnin Jihar Oyo, Alhaji Dauda Shehu ya ce, mun yi wata ganawa ta musamman a tsakaninmu da ’yan kasuwa masu fataucin irin wannan kaya daga jihohin Filato da Kaduna da Kano da Sakkwato.

Ya ce sun amince da yi wa kansu da al’ummar Musulmi adalci wajen sauko da farashin kayan a cikin kwana 30 na watan Azumin Ramadan, domin saukaka wa Musulmi da rage masu radadin tsadar rayuwa a wannan lokaci.

Sai dai ya ce, farashin wadannan kaya za su koma yadda ake sayar da su a baya da zarar watan Azumin ya kare.

Ya ce, “mun yi hakan ne saboda albarkar wannan wata na Ramadan, amma bayan kammala kwana 30 na watan Azumin, ya zama wajibi mu mayar da farashin wannan kaya kamar yadda muke sayarwa a baya domin ci gaba da rage farashin zai iya janyo mana asara.

“Muna daukar matakin rage farashin kayan ne bayan mun rage ribar da ke shiga aljihunmu.

Da yake amsa wata tambaya, Alhaji Dauda Shehu ya ce, “masu sarin irin wannan kaya daga sashen Kudu maso Yamma da suke rububin shigowa cikin wannan kasuwa ta Ibadan a kowane garin Allah Ya waye, mun ba su shawarar daukar matakin rage farashin kayan a garuruwan da suka fito, domin samun sauki ga Musulmi a cikin wannan lokaci.

Ya ce, “tashin farashin irin wannan kaya ba laifin mu ba ne, domin yanayi ne da ya shafi kasa baki daya da ke matukar bukatar ci gaba da addu’o’in rokon Allah samun sauki.”

Alhaji Dauda Shehu ya ce, a yanzu haka ana sauke nau’in irin wannan kaya a cikin manyan motoci uku zuwa biyar a kullum a cikin kasuwar ta Benjamin, inda manya da kananan ’yan kasuwa suke rububin saye domin baje-kolinsu a cikin shagunan cikin gari da masu yawon talla a kan hanyoyin birnin na Ibadan.