Ƙungiyar ƙawancen Sahel na taro karon farko a Nijar

ECOWAS za ta yi taro a Nijeriya a ranar Lahadi domin tattaunawa kan ƙungiyar ta Sahel Alliance.

Ƙungiyar ƙawancen Sahel na taro karon farko a Nijar

A karon farko, ƙasashen Nijar da Mali da kuma Burkina Faso da suka karɓe mulki da tsinin bindiga daga hannun farar hula na gudanar da taron koli a ƙarƙashin ƙungiyar ƙawance ta AES.

Fadar shugaban Burkina Faso ta ce, batun yaƙi da ta’addanci da kuma karfafa hadin gwiwa a tsakanin kasashen su ne batutuwan da za su mamaye zauren tattaunawarsu.

Idan ba a manta ba, shugabannin ƙasashen uku sun kafa kungiyar kawancen yankin Sahel wato AES bayan ficewa daga ECOWAS sakamakon dakatar da su daga harkokin ƙungiyar.

Dama dai ƙasashen sun yanke alaka da tsohuwar uwargijiyarsu Faransa, inda suka karkata alakarsu da kasar Rasha.

Duk shugabannin ƙasashen uku sun bar ƙungiyar ECOWAS a watan Janairu inda suke zargin ‘yar amshin shata ce ta Faransa haka kuma ba ta yin abin da ya dace wurin daƙile masu iƙirarin jihadi.

A watan Maris ne ƙungiyar ta AES ta sanar da shirinta na yaƙi da masu iƙirarin jihadi, duk da cewa ba ta fito ta bayyana hanyoyin da za ta bi ba.

Haka kuma duka shugabannin ƙasashen uku sun ja layi tsakaninsu da Faransar, inda suka kori sojojinta da ke zaune a ƙasashen inda suka ƙulla ƙawance da Rasha.

Kasashen Nijar da Mali da kuma Burkina Faso sun sha fama da matsalolin kungiyoyin da ke gwagwarmaya da makamai a kan iyakarsu wanda ya yi sanadin rayukan dakarun soji da kuma fararen hula da dama.

A gefe guda, su ma shugabannin na ECOWAS za su yi taro a Nijeriya a ranar Lahadi domin tattaunawa kan dangantakarsu da ƙungiyar ta Sahel Alliance.

Cutar Anthrax ta ɓarke a Zamfara

Faston da ke yi wa ’yarsa fyaɗe tsawon shekaru ya shiga hannu

Trump ya rattaba hannu kan gomman dokokin zartarwa

Ƙungiya ta buƙaci rage harajin cinikayya saboda ƙuncin rayuwa