Ƙungiyar Ƙwadago ta shiga yajin aiki kan mafi ƙarancin albashi
NLC ta yi fatali da tayin N60,000 a matsayin mafi ƙarancin albashin ma’aikata.
Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya NLC ta tsunduma yajin aikin sai baba ta gani bayan rashin cimma matsaya da Gwamnatin Tarayya kan mafi ƙarancin albashin ma’aikata.
’Yan ƙwadagon a wannan Juma’ar sun sanar da shiga yajin aikin kai tsaye kan abin da suka kira hawa kujerar naƙi da Gwamnatin Tarayya ta yi na sauya matsayarta kan mafi ƙarancin albashi ma’aikata.
Wannan na zuwa ne a yayin da NLC ta yi fatali da tayin N60,000 a matsayin mafi ƙarancin albashin ma’aikata da Gwamnatin Tarayyar ta gabatar.
Shugaban NLC na ƙasa, Kwamared Joe Ajaero ne ya sanar da hakan a wani taron manema labarai da ya gudana a Babban Ofishin NLC na Ƙasa da ke Abuja.
Kwamared Ajaero ya ce yajin aikin zai fara ne kai tsaye daga ƙarfe 12:00 na daren Lahadi wayewar gari Litinin.