Ƙungiyar Ƙwadago ta yi watsi da N48,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi

NLC ta yi mamakin dalilin da gwamnati da mambobin kamfanoni masu zaman kansu ke tozarta su.

Ƙungiyar Ƙwadago ta yi watsi da N48,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi

Ƙungiyar Ƙwadago NLC ta yi fatali da tayin naira 48,000 da Gwamnatin Tarayya ta gabatar a matsayin mafi ƙarancin albashin ma’aikata a ƙasar.

Mambobin ƙungiyar ta NLC a wannan Larabar su bayyana mamakin dalilin da gwamnati da mambobin kamfanoni masu zaman kansu ke tozarta su da abin da ta bayyana a matsayin tayi mai ban dariya.

Aminiya ta ruwaito cewa a yayin da Gwamnatin Tarayya ta miƙa tayin Naira 48,000, ‘yan ƙungiyoyi masu zaman kansu sun miƙa tayin N54,000.

Sai dai ƙungiyar NLCn ta bayyana adawartwa kan duk tayin da ɓangarorin biyu suka gabatar a wani taron tattaunawa da aka gudanar a babban Ofishin NLC na Labour House da ke Abuja.

Shugabannin ƙwadagon sun ce gwamnati ba ta gabatar da wasu bayanai da za su goyi bayan tayin da ta gabatar ba.

NLC ta yi watsi da ƙara kuɗin kiran waya da data

DSS ta gurfanar da Mahdi Shehu kan zargin ta’addanci

Sojoji sun kashe mataimakin Bello Turji

Harin ’Yan Fashi: Buni ya jajanta wa ’yan kasuwar Ngalda