Ƙungiyar Matasan APC ta faɗi waɗanda suka ɗauki nauyin zanga-zangar matsin rayuwa
An buƙaci matasa su haɗa kai da gwamnati domin cimma burinsu na samun makoma mai kyau.
Ƙungiyar matasan jam’iyyar APC (All Progressive Congress Youth League) a ranar Talata ta ce ‘yan siyasar da suka sha kaye a zaɓen 2023 ne ke da alhakin zanga-zangar da ake yi a faɗin ƙasar.
Zanga-zangar #EndBadGovernance wadda aka fara a ranar 1 ga watan Agusta ta kawo cikas ga harkokin tattalin arziki, musamman a yankin Arewa.
Da yake bayani, shugaban ƙungiyar matasan jam’iyyar APC na ƙasa, Kwamared Olamide Lawal, ya bayyana tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar AAC (African Action Congress) Omoyele Sowore a matsayin jigon waɗanda suka shirya zanga-zangar da sauran waɗanda suka sha kaye a babban zaɓen da ya gabata.
Lawal, wanda kuma shi ne mataimaki na musamman ga gwamnan Jihar Ogun kan harkokin ci gaban matasa, ya bayyana rashin jin daɗinsa kan yadda wasu matasa suka yi kunnen uwar shegu ga kiran da shugaban ƙasar ya yi na kawo ƙarshen zanga-zangar bayan ya yi jawabi ga al’ummar ƙasar.
A cewarsa, “Gayyatar da shugaba Tinubu ya yi na tattaunawa da masu zanga-zangar za ta magance dukkan matsalolin da suke damun su.
“Sun ce muna son shugaban ƙasa ya amsa mana. Ya kuma amsa. Wannan yana nufin ya ji kuka da damuwar kowa”.
Ya buƙaci matasa su haɗa kai da gwamnati domin cimma burinsu na samun makoma mai kyau.
“Ina kira ga dukkan matasan ƙasar nan masu son ci gaba da tsayuwa tsayin daka da bin umarnin Shugaban ƙasa.
“Yana da manufa ta gyara kurakuran da aka yi a baya domin kai Najeriya tudun tsira. Amma zai iya yin cimma hakan ne kawai idan ya samu goyon baya,” in ji Lawal.
Ya kuma ja kunnen ‘yan siyasa da kada su bari muradin kansu su kawo cikas ga zaman lafiya da ci gaban ƙasa.