Ƙungiyoyin ƙwadago sun buƙaci Tinubu ya mayar da Fubara kan kujerarsa
Ƙungiyoyin sun matakin da Tinubu ya ɗauka ya saɓa wa sashe na 2 da na 305 na kundin tsarin mulki.

Ƙungiyoyin Ƙwadagon Najeriya, NLC da TUC, sun yi Allah-wadai da matakin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya ɗauka na sanya dokar ta-ɓaci a Jihar Ribas.
Ƙungiyoyin sun soki dakatar da Gwamna Siminilayi Fubara, mataimakiyarsa, da ’yan majalisar dokokin jihar.
- Goman Ƙarshe: Dama ta ƙarshe ga mai neman rahamar Allah
- Matatar Dangote ta dakatar da sayar da fetur a Naira
A wata sanarwa da suka fitar ranar Laraba, ƙungiyoyin bitu sun bayyana cewa wannan mataki ya saɓa wa kundin tsarin mulkin Najeriya, musamman sashe na 2 da 305 na dokar 1999 da aka yi wa kwaskwarima.
Sun ce wannan mataki ne da ka iya tauye ikon zartarwa, tare da zama barazana ga dimokuraɗiyya a Najeriya.
A ranar Talata ne, Shugaba Tinubu ya sanar da sanya dokar ta-ɓaci a Jihar Ribas, inda ya bayyana cewa rikicin siyasar jihar yana barazana ga zaman lafiya da tsaron al’umma.
Wannan mataki ya janyo ce-ce-ku-ce a faɗin Najeriya, inda mutane da dama ke ganin hakan bai dace da kundin tsarin mulki ba.
Ƙungiyoyin NLC da TUC sun buƙaci Shugaba Tinubu da ya gaggauta janye wannan mataki, don kada ya jefa Najeriya yanayin saɓa wa doka a nan gaba.