Ƴan sanda sun taro ƴan daba ƙwallon kafa a Kano
Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce za ta buga ƙwallon ƙafa da ƴan daban da suka addabi birnin Kano a wani ɓangaren na ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya. Kwamishinan ƴan sanda Muhammad Useni Gumel ne ya bayyana haka lokacin da yake holin wasu mutane 108 da ake zarginsu da aikata laifuffuka lokacin bikin Sallah […]
Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce za ta buga ƙwallon ƙafa da ƴan daban da suka addabi birnin Kano a wani ɓangaren na ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya.
Kwamishinan ƴan sanda Muhammad Useni Gumel ne ya bayyana haka lokacin da yake holin wasu mutane 108 da ake zarginsu da aikata laifuffuka lokacin bikin Sallah Babba.
CP Gumel ya ce, “Zamu fito da sababbin hanyoyin da zamu tabbatar waɗannan ƴan dabar sun gyara halayaensu sun zama mutanen kirki.
’Yan daba sun daddatsa dan sanda a Kano
’Yan daba sun kashe mutum, sun jikkata wasu a wurin zabe
“Zamu shirya gasar wasanni tsakaninmu da su. Zamu buga ƙwallon ƙafa da kuma wasannin cikin rufaffen ɗaki.”
Harkar daba dai ta ƙara tsamari a birnin Kano da kewaye tun lokacin zaɓen 2023.
A baya-bayan nan ma ƴan daba sun daddatsa wani ɗan sanda a Kano lokacin da suke faɗa da junansu.
Ya gayyaci iyayen daba
Dangane da haka ne kwamishinan ƴan sandan ya gayyaci wasu iyayen daba da suka yi ƙaurin suna wurin tada hatsaniya a Birnin Kano da su miƙa kansu ga ofisoshin ƴan sanda na kusa da su.
Ya kuma yi gargaɗin cewa idan ba su kai kansu ba, rundunar za ta bi su ta kama kuma ta gurfanar da su gaban shari’a domin ɗanɗana sakamakon abin da suke aikatawa.
Waɗannan iyayen dabar sun haɗa da Burakita na unguwar Ɗorayi Ƙarama, Messi na Kan Tudun Dala, Ɗan Boss na Dala Maƙabarta, da Ado Runto na Tudun Fulani.
Akwai kuma Baffa Killer na Mazaunar Tanko, Kamilu Duna na unguwar Adakawa, Chile Mai Doki na Tudun Fulani da Uzaifa na Unguwar Yola.
Sai kuma Hantar Daba na Kwanar Ɗiso, Bahago na Maƙabarta Kuka Bulukiya, Nasiru Naso na Ƙofar Wambai da Nazifi Nanaso na Zango.
Sauran su ne Sharu Gambo na Sharifai, Sharu Ali na Sharifai, Ma’aruf Goma na Hanga da Zubairu Mai Dala na unguwar Yalwa.