Ɓarawo mai asirin barci ya shiga hannu a Katsina

Bayan zuwa gidan ne Musa Rabi’u wanda ake zargin yana da asirin barci ya shiga ya lalube duk ɗakunan gidan inda ya ɗauko wata jakar kuɗi da ke ɗauke da Naira milyan biyu da kuɗin ƙasar Libya

Ɓarawo mai asirin barci ya shiga hannu a Katsina

Wani matashi mai suna Musa Rabi’u da ake zargi da yi wa mutane asirin sa barci a duk lokacin da ya shiga gidajensu don yin sata ya faɗa komar ’yan sandan a Jihar Katsina.

Musa mai kimanin shekaru 20 ya shiga hannu ne sanadiyar haɗa kai da wasu abokan harkalla —Basiru Ayuba mai shekara 22 da Muhammad Musa mai shekara 45 da ke zaune a garin Babban Mutun na Ƙaramar Hukumar Ɓaure a jihar ta Katsina.

Haka kuma, an kama wani Abubakar Abdullahi wanda shi ne suke tare da Musan da ke zama a garin Daura a matsayin ɗalibi.

Rahotanni sun ce ababen zargin huɗun sun sanya wani Muhammad Musa a matsayin jagoran da ke bayar da shawarar kitsa yadda za a riƙa sace-sacen a gidajen jama’a.

Aminiya ta ruwaito cewa ababen zargin dai sun je gidan wani mai harkar kuɗi ta POS mai suna Rabi’u Umar a garin na Babban Mutun domin yi masa fashi.

Bayan zuwa gidan ne Musa Rabi’u wanda ake zargin yana da asirin barci ya shiga ya lalube duk ɗakunan gidan inda ya ɗauko wata jakar kuɗi da ke ɗauke da Naira milyan biyu da kuɗin ƙasar Libya Dinaru 15 da wayar hannu ƙirar Tecno Camon 20 ba tare da wani a cikin gidan ya motsa ba.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, Basiru Ayuba da Abdullahi Abubakar sun fara haɗuwa ne a gidan gyaran hali, yayin da shi Muhammad Musa ya zamo jagora kuma mai ba su shawara duk kuwa da cewa ya san suna wannan ɗabi’a ta sata.

Sai dai Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Katsina, ASP Abubakar Sadiƙ Aliyu wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce sun yi nasarar kama waɗannan ababen zargin tare da tsamo jakar da ke ɗauke da kuɗin wadda suka jefa rijiya bayan sun gama kasafin kuɗin a tsakaninsu.

Kakakin ya ƙara da cewa, da zarar sun kammala bincike za su tura su zuwa ƙuliya manta sabo don girbar abin da suka shuka.