Ɓarayi sun sace ragon layya a Abuja

Ɓarayin sun sace ragon ne lokacin da mai gidan baya nan.

Ɓarayi sun sace ragon layya a Abuja

Wasu ɓarayi sun haura gidan wani mutum mai suna Malam Mundi Shuaibu, inda suka yi awon gaba da ragon layyarsa a Unguwar Sabon-Tasha da ke Abuja.

Gidan wanda aka sace wa ragon ya haɗa katanga da kasuwar shanu wadda ke ci duk bayan kwana biyar a sati.

Wani maƙocin mutumin, Abdullahi Ahmed, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Asabar da misalin ƙarfe 1:12 na rana bayan mai gidan ya fita.

Ya ce, “Lokacin da maƙocina ya dawo da misalin ƙarfe 4 na yamma, ya je inda ya ɗaure ragonsa, sai ya tarar babu komai.”

Ahmed ya shaida wa Aminiya cewar, mai ragon ya ce ya sayo shi ne kan Naira 215,000 a makon da ya gabata don yin layya da shi.

Har yanzu babu wani martani daga rundunar ‘yan sandan Abuja, kan lamarin zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.