Ɓarayin buhun abincin tallafin MDD 1,840 sun shiga hannu
An kama wasu direbobi da suka sace buhu 1,840 na abincin tallafin Majalisar Ɗinkin
An kama wasu direbobi biyar da suka sace buhu 1,840 na abincin tallafin Majalisar Ɗinkin Duniya a Najeriya.
Dubun direbobin ta cika ne a hanyarsu ta kai buhunan alkaman da suka sace Jihar Kano daga tashar jiragen ruwa na Fatakwal da ke Jihar Ribas.
Ana zargin direbobin sun sace buhunan abincin tallafin da Shirin Abinci na Majalisar Ɗinkin Duniya (WFP) ne, a cewar Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Ribas, Jimoh Moshood.
Kwamishinan ya ce ana neman wasu direbobi biyu da wasu mutane da suka tsere kan satar abincin tallafin. Ya ƙara da cewa binciken ma da muhimmanci domin akwai buhunan alkaman sama da 600 da suka yi layar zana daga cikin adadin.
Ya ce an kwace motoci biyu da aka yi amfani da su wajen aikata satar sannan kotu ta ɗaure masu laifin.
Ya ƙara da cewa an mika wa hukumar WFP buhunan alkama guda 1,238 da aka kama, ragowar 602, ana ci gaba da bincike domin gano su.