‘Ɓarkewar cutar kwalara a jihohin Yarabawa ba ta da alaƙa da matsugunin Hausawa’
An yi kira ga Hausawa a dukkan jihohin Yamma su kasance masu tsabtace muhallansu.
Sarkin Hauswan Garin Ibafo da ke Jihar Ogun, Malam Shehu Ɗanyaro Usman ya yi watsi da zargin da wasu mutane ke yi cewa ɓarkewar cutar kwalara a jihohin Yarabawa ta samo asali ne daga matsugunin Hausawa na Ibafo, abin da ya ce zance ne na soki burutsu marar tushe.
Sarkin Hausawan ya ce cutar kwalara cuta ce da ke da nasaba da rashin tsabtar muhalli, kuma cuta ce da za ta iya ɓarkewa a kowane wuri musamman wuri marar tsaba.
Sarkin Hausawan ya ce, “Mu dai a garin Ibafo alhamdulilLahi har yanzu ba mu samu rahoton ɓullar cutar ba, kuma ba ma fata ta ɓulla, saboda muna yin duk abin da ya kamata na ganin mun tsabtace muhallanmu saboda gudun kamuwa da cututtukan da ke da nasaba da rashin tsabta ba cutar kwalara kawai ba.”
Sarkin Hausawan ya yi kira ga Hausawa mazaunin garin Ibafo da dukkan jihohin Yamma su kasance masu tsabtace muhallansu daidai gwargwado domin gudun ɓarkewar cuta.
Ya kuma yi kira da mutane su gaggauta zuwa asibiti a duk lokacin da suka ga alamun ɓullar kowace cuta don ɗaukar matakan kariya.
Ya yaba wa hukumomin lafiya na Jihar Ogun da na ƙasa bisa matakan kariya da suke bayarwa ga al’umma daga wannan cuta ta kwalara.