Masu zanga-zanga da tutar Rasha sun fasa banki a Kaduna
Ɓata garin sun lalata motoci da dukiyoyin ma’aikatan bankin.
Wasu ɓata gari ɗauke da tutar ƙasar Rasha sun shiga cikin masu zanga-zangar yunwa, tare da fasa wani banki a Jihar Kaduna.
Zanga-zangar dai ta rikiɗe zuwa tashin hankali a rana ta biyar a jihar, inda wasu ɓata gari suka kai hari banki a yankin Tudun Wada na Kaduna.
- Tinubu na ganawa da shugabannin tsaro a Aso Rock
- An kama tela da wasu 30 kan zanga-zanga da tutocin Rasha a Kano
Ɓata garin sun lalata motocin ma’aikatan bankin sannan suka sace kayayyakin kuɗi masu tarin yawa.
Gwamnan jihar, Uba Sani, ya sanya dokar hana fita ta sa’o’i 24 a yankin Kaduna da Zariya, biyo bayan tashe-tashen hankula da aka samu.
Tun daga wannan lokaci, jami’an tsaro suka shiga tarwatsa ɓata garin da ke ƙoƙarin satar kayan mutane da kuma tabbatar da zaman lafiya a jihar.
A ranar Alhamis ne, aka kama aƙalla mutum 25 da suka fasa shagunan mutane tare da sace musu kayayyaki a ranar farko ta zanga-zangar yunwa a jihar.
Zanga-zangar ta rikiɗe zuwa tashin hankali a yankin Kaduna ta Arewa da wasu sassan Kaduna ta Tsakiya, yayin da yankin Kaduna ta Kudu ke cikin kwanciyar hankali.
Tuni tituna a Jihar Kaduna, sun zama fayau babu mutane tun bayan saka dokar hana fita.
Mazauna Kaduna sun yaba wa gwamnan jihar bisa saka dokar.