Ɓata-gari sun daka wawa a motar dakon abinci ta BUA a Zariya

Ɓata-garin sun wawashe duk katan-katan na kwalayen taliya da motar ke ɗauke da su.

Ɓata-gari sun daka wawa a motar dakon abinci ta BUA a Zariya

Wasu ɓata-gari sun daka wawa a wata motar dakon kayan abinci ta Kamfanin BUA a unguwar Dogarawa da ke babban titin Zariya zuwa Kano.

Ɓata-garin dai kamar yadda wakilinmu ya ruwaito sun yi awon gaba da katan-katan na kwalayen taliya da motar ke ɗauke da su da maraicen wannan Juma’ar.

Ɓata-garin sun afka wa motar ne da misalin karfe 3.15 na rana sa’ilin da direban motar ya tsaya don gudanar da sallah.

Wani ganau ya shaida wa Aminiya cewa direban ya tsaya ne don gudanar da Sallah, inda nan take, ɓata-garin suka afka wa motar kuma suka sa wawaso.

Ya kara da cewa ɓata-garin sai da suka wawushe dukkan katan-katan ɗin taliyar da motar ke ɗauke da shi kafin daga bisani kowa ya arce da abin da ya samu.

Wakilinmu ya ruwaito cewa daga baya dai ’yan sandan da suka hallara domin ɗauka mataki a wurin da lamarin ya faru sun samu nasarar cafke mutane biyar daga cikin ɓata-garin.

Gwamnatin Yobe ta tallafa wa magidanta 53,000 da N3.91bn a 2024

Uwargidan Sanata Goje ta tallafa wa mata da matasa a Gombe

An kama bokaye 2 kan zargin yi wa shugaban Zambiya asiri

Kirsimeti: FRSC ta aike jami’ai 1,539 zuwa Kano