Ɗalibai a jihohi 14 na cikin haɗarin ’yan bindiga — Gwamnatin Tarayya
Mun tattara bayanai da za su taimaka wajen kai wa makarantun ɗauki.
Gwamnatin Tarayya ta fitar da jerin jihohin 14 da makarantunsu ke cikin haɗari da kuma raunin da za a iya kai musu hari daidai lokacin da ’yan bindiga ke ci gaba da kutsawa makarantu suna sace ɗalibai.
Shugabar hukumar samar da kuɗaɗen bayar da kariya ga makarantu na ƙasar, Hajiya Halima Iliya ce ta bayyana hakan yayin tattaunawa da manema labarai.
A shekarar 2014 ne aka kafa hukumar bayan sace ɗaruruwan ɗaliban makarantar Chibok da ke Jihar Borno.
Hajiya Halima ta ce jihohin da wasu makarantunsu ke cikin haɗarin sun haɗa da Adamawa, Bauchi, Borno, Benuwe, Yobe, Katsina, Abuja, Kebbi, Sakkwato, Filato, Zamfara da ƙarin wasu guda 3.
A cewar Hajiya Halima, hukumar ta tattara bayanai da za su taimaka wajen kai wa makarantun ɗauki.
Bayanin hukumar na zuwa ne kasa da mako guda bayan da ’yan bindiga suka yi garkuwa da yaran firamare da sakandire kusan 300 a ƙauyen Kuriga da ke Jihar Kaduna.
Kwana guda bayan nan kuma ’yan bindigar suka sace ɗaliban tsangaya 15 a Karamar Hukumar Gada ta Jihar Sakkwato.
Sace-sacen sun biyo bayan sace wasu ɗaruruwan ’yan gudun hijira a Ngala da ke Jihar Borno da ake zargin ’yan Boko Haram da aikatawa.