Ɗaliban kiwon lafiya da aka sace a Benuwe sun kuɓuta — ’Yan sanda

Babu ko kobo da aka biya saɓanin wasu rahotanni da ke cewa an bayar da kuɗin fansa.

Ɗaliban kiwon lafiya da aka sace a Benuwe sun kuɓuta — ’Yan sanda

Rundunar ’yan sandan Nijeriya ta tabbatar da cewa an kuɓutar da ɗaliban kiwon lafiya aƙalla 20 da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a Jihar Benuwe.

’Yan sandan sun kuma tabbatar da cewa ɗaliban sun kuɓuta ne ba tare da biyan ko asi ba saɓanin wasu rahotanni da ke cewa an bayar da kuɗin fansa kafin a sake su.

Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Nijeriya, ACP Olamuyiwa Adejobi ne ya tabbatar da wannan labari yayin ganawa da manema labarai a safiyar wannan Asabar.

“Muna tabbatar muku cewa an sako ’yan uwanmu ɗaliban kiwon lafiya 20 maza da mata da ma sauran wasu ’yan Nijeriya ranar Juma’a, 23 ga watan Agusta waɗanda aka yi garkuwa da su a dajin Ntunkon da ke Jihar Benuwe.

“Muna kuma jaddada cewa babu ko kobo da aka biya saɓanin wasu rahotanni da ke cewa an bayar da kuɗin fansa kafin a sake su.

“A haƙiƙanin gaskiya an ceto su ta hanyar amfani da dabarun aiki da ƙwarewa.

“Muna godiya ga jami’an tsaro da mazauna yankin da lamarin ya faru, da kuma ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan sha’anin tsaro bisa jajircewarsu.”

Aminiya ta ruwaito cewa, ɗalibai 12 na Jami’ar Maiduguri ta Jihar Borno da takwas na Jami’ar Jos ta Jihar Filato ne suka faɗa komar masu garkuwa da mutanen a Jihar Benuwe.

Rundunar ’yan sandan Jihar Benuwe ta tabbatar da sace ɗaliban a ranar Alhamis, 15 ga watan Agustan nan tana mai cewa lamarin ya faru ne a kan hanyar Otukpo zuwa Enugu.

Lamarin ya rutsa da ɗaliban da ke kan hanyarsu ta halartar taron Ƙungiyar Ɗaliban Likitanci na shekara-shekara da za a gudanar a Jihar Enugu.

Arewacin Nijeriyar dai ya yi ƙaurin suna wajen ayyukan ’yan bindiga da ke garkuwa da mutane domin samun kuɗin fansa, musamman ta hanyar tare tituna da kuma kai wa kauyuka farmaki daga lokaci zuwa lokaci.

NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Suka Sa Farashin Citta Ta Yi Tashin Gwauron Zabo

Wike ya ƙwace filayen jiga-jigan ’yan siyasa a Abuja

Gwamnoni sun ƙi amincewa da ƙara harajin VAT

Matashi ya kashe mahaifinsa kan N5,000 a Delta