Ɗalibar Jami’ar Abuja Da Ta Ɓace Ranar Juma’a Ta Rasu

Iyayen wata dalibar aji hudu a Jami’ar Abuja, Murjanatu Zubairu, da ta bace ranar Juma’a, sun ce ta mutu.  Kawun marigayiyar, Alhaji Zubairu Jibrin Yewuti ne ya tabbatar wa wakilin mu da rasuwarta a ranar Litinin. Ya ce iyayen Murjanatu sun  sanar da shi cewa bayan gudanar da bincike mai zurfi sun gano cewa ta […]

Ɗalibar Jami’ar Abuja Da Ta Ɓace Ranar Juma’a Ta Rasu

Iyayen wata dalibar aji hudu a Jami’ar Abuja, Murjanatu Zubairu, da ta bace ranar Juma’a, sun ce ta mutu. 

Kawun marigayiyar, Alhaji Zubairu Jibrin Yewuti ne ya tabbatar wa wakilin mu da rasuwarta a ranar Litinin.

Ya ce iyayen Murjanatu sun  sanar da shi cewa bayan gudanar da bincike mai zurfi sun gano cewa ta rasu ne a wani mummunan hatsarin mota a yammacin ranar Juma’a a kan hanyar Lugbe.

A cewarsa, iyayen yarinyar sun gano gawarta ne a dakin ajiye gawarwaki na Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abuja da ke Gwagwalada lokacin da suka je asibitin domin tambayar ko an kawo ta ba lafiya ko wani abu makamancin haka.

Alhaji Zubairu ya ce, “iyayenta sun kira ni sun sanar da ni cewa ta rasu ne a hatsarin mota da ya rutsa da ita a babban titin Lugbe zuwa filin jirgin Abuja.”

Kwamandan hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) na shiyyar Lugbe, Sunday Ajokotola, ya tabbatar da cewa mutane 10 ne hatsarin mota ya rutsa da su, inda mace daya da maza uku suka kone kurmus a ranar Juma’ar da ta gabata.

Tinubu ya yi naɗin sabbin muƙamai huɗu

Majalisar Zartarwa ta amince da kusan Naira tiriliyan 50 Kasafin Kuɗin 2025

Tinubu ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa

HOTUNA: Ana shirye-shiryen jana’izar marigayi Lagbaja