An kashe manyan alƙalai 2 a harabar Kotun Ƙolin Iran
“Alƙalai uku aka kai wa harin, biyu daga cikinsu sun yi shahada, na ukunsu kuma ya samu rauni. Maharin kuma ya kashe kansa.”
Wani ɗan bindiga ya buɗe wa alƙalai wuta inda ya halaka mutum uku a harabar Kotun Ƙolin ƙasar Iran.
A safiyar Asabar ne maharin ya buɗe musu wuta, inda ya aika alƙalai biyu lahira, da wani mai tsaron lafiyan alƙalai. Wani alƙali na ukun kuna ya tsallake rijiya da baya da raunin harbi.
Ma’aikatar Shari’a ta ƙasar Iran, ta bayyana cewa ɗan bindigar ya kashe kansa bayan harin.
Ta sanar a shafinta cewa, alƙalan da aka kashe su ne: Mohammad Moghiseh da Ali Razini.
- ’Yan Yahoo sun harbe jami’in EFCC har lahira a bakin aikinsa
- Gaza: Yadda za a yi musayar fursunonin Palasdinawa da Isra’ila
Ta ci gaba da cewa, “Alƙalai uku aka kai wa harin, biyu daga cikinsu sun yi shahada, na ukunsu kuma ya samu rauni. Maharin kuma ya kashe kansa.”
Kawo yanzu dai ba a gano dalilin harin ba, amma a baya shafin ’yan adawar ƙasar ya sanar cewa Mohammed Moghiseh yana cikin masu sauraron shari’ar fursunonin siyasa.