Ɗan ci-ranin Arewa ya zama shugaban kamfanonin haƙar ma’adinai a Kudu
A wata hira da Aminiya ta yi da Adamu Mai Aful a matsayinsa na Babban Daraktan Kamfanin Dokkal-Khairu Nigeria Limited ya ce, akwai ma’aikata fiye da 200 da suke aiki a ƙarƙashin kamfanin. Ya fara ne da bayanin yadda yake sha’awar karanta irin labaran da Jaridar Aminiya ke bugawa, inda ya ce, “na fara sha’awar […]
A wata hira da Aminiya ta yi da Adamu Mai Aful a matsayinsa na Babban Daraktan Kamfanin Dokkal-Khairu Nigeria Limited ya ce, akwai ma’aikata fiye da 200 da suke aiki a ƙarƙashin kamfanin.
Ya fara ne da bayanin yadda yake sha’awar karanta irin labaran da Jaridar Aminiya ke bugawa, inda ya ce, “na fara sha’awar karanta labaran da suke fitowa a shafukan Jaridar Aminiya a kowane mako ne tun ina da ƙuruciya a mahaifata da ke garin Kwami, hedikwatar Ƙaramar Hukumar Malam Sidi a Jihar Gombe.”
Matashin ɗan kasuwa ya ce, “sha’awar karanta labaran Jaridar Aminiya ne ya sa na ƙulla yarjejeniya da ofishin Kamfanin Media Trust da ke buga Jaridar Aminiya a Legas a kan yadda za su riƙa tura min kwafi masu yawa na Jaridar Aminiya zuwa garin Ile-Ife, inda yaran da ke aiki a babban ofishina za su riƙa sayarwa ga al’ummar Hausawa mabuƙatan jaridar.”
Ya nuna matuƙar farin ciki da yadda yarjejeniyar ta fara aiki nan take, inda Kamfanin na Media Trust ya fara aika wa da kwafe 30 na Jaridar Aminiya mai ɗauke da labarin rasuwar Sarkin Hausawan IleIfe a shafinta.
Ya bayyaan cewa, nan take aka sayar da jaridar ga mabuƙata ’yan Arewa ba tare da ta yi kwantai ba.
A kan yadda a matsayinsa na ɗan Arewa ya yi fice a harkar haƙar ma’adini har ya zama Shugaban Ƙungiyar Kamfanonin Ƙasa Masu Haƙar Ma’adinai a Jihar Osun, sai Alhaji Adamu ya kaɗa baki ya ce, “da farko dai zan so in yi maka bayanin yadda na fito yawon ci-rani daga garin Kwami mahaifata a Jihar Gombe.
Na fito ne da jarin kuɗi Naira dubu 25 a hannuna, inda na yada zango a Jihohin Kaduna da Legas da Ogun da Ondo da Ekiti. A ƙarshe zaman dindindin ya kama ni a garin Ile-Ife cikin Jihar Osun. Duka waɗannan jihohin da na ambata na yi amfani da ɗan jarin kuɗi ne wajen gudanar da ƙananan harkokin kasuwanci. Misali a Jihar Ondo, na shiga sana’ar sayar da doya ce.
Da zarar kakar doya ta janye sai in koma shiga gonakin lemon zaƙi, inda muke ƙulla ciniki a tsakaninmu da manoman da muke sayan duka lemon da suke maƙale a rassan bishiyoyi.
A lokacin da na tare a garin Ile-Ife, na fara da fataucin katon-katon na tufa ne daga garuruwan Ibadan da Legas. Shi ne dalilin da ake kira na da sunan Adamu Mai Aful. A game da amsar tambayarka kuwa, Allah ne Ya haɗa ni da wani Basine ɗan ƙasar China da yake sana’ar zinare, yana zuwa sayan Aful a teburin da na baje haja a unguwar Sabo Ile-Ife.
Shi ne ainihin mutumin da ya tsoma ni cikin harkar haƙar ma’adini, inda ya fara kawo min zinare daga daji, yana sayar min da sauƙi. Ni kuma sai in ɗauka zuwa Arewacin ƙasa, musamman Jihar Kano, inda nake sayarwa, ina samun riba har zuwa yanzu da Allah Ya sanya wa sana’ar albarka”.
Adam mai Aful ya ƙara da cewa, “yanzu haka akwai matasan yara fiye da 200 da suke aiki a ƙarƙashin kamfanina na Dokkal-Khairu Nigeria Limited da nake biyan su albashin sama da Naira miliyan 3 a kowane wata. Kaɗan ke nan daga labarin yadda Allah ya ɗaukaka ni zuwa matsayin da nake ciki a yanzu da kamfanonin da muke aiki tare suka zaɓe ni a matsayin Bahaushe na farko da ya zama Shugaban Ƙungiyar Kamfanonin Haƙar Ma’adinai ta Jihar Osun.”
Matashin ya ƙara da cewa, “muhimmin aiki da na fara yi a matsayin shugaban ƙungiyar shi ne kusantar mahukumta domin tabbatar da ganin kowane kamfani a cikin ƙungiyarmu ya samu lasisin izinin gudanar da wannan aiki da zai kare mutuncinmu daga yawan zargin da ake yi mana cewa, muna yin aikin ne ta haramtacciyar hanya.
Wannan mataki da na ɗauka ya yi tasiri sosai, inda gwamnatin jihar ta janyo mu a jiki, muke cin moriyar zamantakewa ta fannoni daban-daban.”
Dangane da irin nau’in ma’adanin da ake haƙowa a Jihar Osun sai ya ce, “mafi yawanci zinare ne muke haƙowa kuma dillalai daga Abuja da Kano suna zuwa, suna saya a ranakun Laraba da Lahadi na kowane mako. Daga can kuma su tafi da su zuwa Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta Dubai.”