Ɗan fashi ya yi wa ɗaliban jami’a uku fyaɗe

Yi wa ɗalibai mata uku na Jami’ar Jihar Kwara fyaɗe tare da fashi da makami

Ɗan fashi ya yi wa ɗaliban jami’a uku fyaɗe

Kotu ta tsare wani ɗan fashi da ya yi wa ɗalibai mata uku na Jami’ar Jihar Kwara fyaɗe.

Matashin da dubunsa ta cika yi wa ɗaliban fyade ne a yayin wani fashi a ɗakunan kwanan ɗalibai mata a cikin dare.

Ya yi musu wannan aika-aika tare da yunƙurin kisa ne a daƙinsu kwanan ɗalibai mata da ke wajen harabar jami’ar a yankin Malete a ranar 2 ga watan Disamba, 2024.

A yayin gurfanar da matashin a gaban Kotun Majiatare ta Jihar Kwara da ke birnin Ilorin, an tuhume shi da yin amfani da makami wajen yi wa ɗaliban munanan raunuka, tare da yi musu fyaɗe da kuma sace wayoyin iPhone 13 PronMax da iPhone 11 Pro Max.

“Kana gab da kashe ɗaya daga cikinsu ne aka kawo musu ɗauki, kuma bincike ya gano cewa kai ɗan ƙungiyar asiri ne tun shekarar 2020, kuma ƙungiyarku ta Aiye, ta yi ƙaurin suna wajen yin fashi da makami da aikata kisa da kuma yi wa ɗalibai mata fyaɗe,” kamar yadda ɗan sanda mai gabatar da ƙara, Nasiru Yusuf, ya karanta a takardar zargin matashin ɗan shekara 26.

Daga nan alƙalin kotun, Majistare Sa’idu ya ba da umarnin tsare wanda ake zargin tare da ɗage shari’ar zuwa ranar 20 ga watan nan na Fabrairu, 2025.